Kano Ta Samar Da Nagartattun Damammakin Cin Nasarar Inganta Tattalin Arziki – Gawuna

Gwamnatin Jihar Kano zata ci gaba da samar da ingantattun damammaki, domin tabbatar da sake farfado da harkokin tattalin arzikin Jihar Kano. Hakan na kunshe cikin jawabin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawna lokacin da ya karbi bakuncin babban manajan Hukumar tsare tsaren fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje Farfesa Adesoji Adesugba wanda ya ziyarci fadar Gwamnatin Jihar Kano cikin makon da ya gabata. Kamar yadda daraktan yada labaran mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADERSHIP A YAU LAHADI

Dakta Gawuna ya jadadda cewa batun kirkiro sabbin dabaru  ne babban abinda wannan Gwamnati ke mayar da hankali akai, wanda ake fatan cin nasarar sa ta hanyar zuba hannun jari da kuma sake fasalin tsare tsare da Jihar Kano ta kirkiro.

“Bayar damar zuba hannun jari  zai ci gaba da zama wani tsari da mu ka bai wa muhimmanci kwarai da gaske, kamar yadda shirin ke samar da ayyukanyi wanda shi ne kashin bayan  kowane kyakkyawan jagoranci,” in ji Gawuna.

Daga nan sai ya tabbatar da cewa, bangaren da Jihar Kano ke da kyakkyawan fata akansa,  zamu ci gaba da hada hannu da hukumar shirya fiton kayayaki  domin  samun nasarar harkokin kasuwanci a Jihar Kano.

Ya kara da cewa, “ tare da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Jihar Kano da cibiyar cinikin, akwai manyan nasarori da aka cimma ta fuskar abubuwanda aka dora alhakinsu akan Gwamnatin Jihar Kano.”

Mataimakin Gwamnan ya kuma bukaci babban Manajan da cewa, cibiyar ciniki ta shiyyar Kano ta bujiro da shirin wayar da kan jama’a, domin sanar da al’umma ayyukan wannan Hukuma da sauran aikace aikace da ta ke gudanarwa.

Saboda haka sai ya bukaci al’umma a Jihar Kano da cewar suyi amfani da damammakin da aka basu domin tabbatar da  shiga cikin tsare tsaren wannan hukuma ka-in-da-na’in.

Tunda farko a na sa jawabin Manajan Darakatan Hukumar harkokin fita kayayyakin Farfesa Adesoji Adesugba ya sanar da mataimakin Gwamnan cewa, zuwansa Jihar Kano na cikin  tsare tsaren da hukumar ke gudanarwa a fadin kasar nan.

Farfesa Adesoji Adesugba ya ci gaba da cewa kamar ko da yaushe yadda Jihar Kano ke zaman cibiyar ciniki a fadin kasar nan, har yanzu a na fatan ganin Jihar Kano ta ci gaba da bayar da goyon baya ga wannan Hukuma, domin samun cikakken sakamakon da ake fata.

“Kansacewar Jihar Kano a matsayin cibiyar ciniki tana da babban matsayi na amfana da dukkan damammakin da wannan hukuma ke aiwatarwa, don haka akwai bukatar  samun ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai wannan Gwamnati  kamar yadda aka baiwa wanda muka gada,” in ji shi.

Exit mobile version