Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

Gidauniyarsa Ta ‘Charity’ Ta Raba Tallafi Ga Masu Bukata Na Musamman

Daga Abdullahi Muh’d, Kano

Shugaban Gidauniyar ‘Charity’ mai rajin tallafa wa matasa da mabukata a karkashin jagorancin Kansila Mazabar Guringawa dake karamar Hukumar Kumbotso Hon. Muslihu Yusif Ali, wanda ya ke da mataimaka 18, ta kaddamar da raba Ttallafi ga masu bukata ta musamman dake mazabarsa, inda ya sadaukar da albashinsa an farko, don yin hakan.
Wannan na cikin kokarin wakilin al’ummar Mazabar Guringawa na ganin al’umma sun amfana da wakilcinsa.
Hon. Muslihu Ali shi ne Kansila na farko kuma wanda ya zama abin misali wanda ya sadaukar da albashinsa domin tallafa wa masu bukata ta musamman dake wannan mazaba da sauran fannonin da ke bukatar taimakon gaggawa.
Ya ce, “bisa la’akari da yadda barace-barace suke zama barazan ga cigaban jama’armu, hakan ta sa na sadaukar da albashinna da na mashawartana na watan da muke ciki, domin samar da jari ga masu bukata ta musamman, wadanda za su fara sana’ar sayar da takunkumin fuska, domin dogaro da kansu.”
Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin bikin raba tallafin jarin sayar da takunkumin rufe fuska, Shugaban karamar Hukumar Kumbotso, wanda mataimakinsa Alhaji Shamsu Sa’ad Kademi ya wakilta, ya bayyana cewa, “muna alfahari da wannan kansila bisa bijiro da abubuwan nagari da suke sa ake kallon karamar Hukumar Kumbotso a matsayin fitilar cigaban al’umma.”
Farfesa Jibrin Isa diso, malami a Jami’ar Bayero kuma wanda makaho ne, cewa ya yi, abinda ya dace kenan ya jawo masu bukata ta musamman jiki, domin tafiyar tare.
Ya ce, ‘wannan kokari na kansila abin alfahari ne gare mu, musamman koyar da sana’o’i, domin magance barace-barace a tsakanin mabukata.”
Farfesa diso ya bukaci gwamnati ta sake dawo da kyakkawar manufar taimaka wa masu bukata ta musamman, ba dogaro da basu sadaka ba. Don haka sai ya yi kira ga saura masu rike da madafun ikon da su yi koyi da wannan abin alhairi na Hon. Muslihu Yusif Ali ya ke yi. Ya kuma bukaci karamar Hukumar Kumbotso ta fara dabbaka wannan kyakkyawan niyya, domin zama abar misali.
Mashawarciya Gwamna Kan harkokin masu bukata ta musamman, Alhaji Tasi’u Garko, cewa ya yi, wannan rana ce ta musamman, inda ya ce, “Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya shelanta batun ilimi kyauta. Saboda haka na yi alkawarin taimaka wa wannan tsari, kuma za mu tabbatar da cikar burinka, za mu dauki matakin kan duk wanda ya sauka daga kan wannan kyakkyawar niyya ta wannan kansila.”
Dagacin Ja’o’ji, Alhaji Sule Sha’aibu, ya jinjina wa kokarin wannan wakili, wanda ya kira da jajirtaccen wakili, wanda ya zama zakaran gwajin dafi kuma abin koyi wanda suke alfahari da wakilcinsa. Daga nan sai ya bukaci wadanda suka rabauta da wannan tallafi da su yi kyakkyawan amfani da shi.
Sarkin Malaman Masarautar Gaya, Sheikh (Dr.) Yusif Ali, ya yi dogon bayani kan amfanin taimaka wa masu bukata ta musamman, wanda ya ce, akwai gagarumin lada daga Allah. Ya cigaba da cewa, lallai akwai bukatar cigaba da taimaka wa bayin Allah. Daga nan sai ya rero wasu baitukan wakokin dake nuna amfanin taimaka wa masu bukata ta musamman.
A lokacin bikin raba tallafi da masu bukata ta musamman da suka hada da makafi, guragu da sauransu, inda suka yi hafzi da tallafin takunkumin fuska, domin sayarwa, kuma ya zama jari gare su.
An dai gudanar da wannan taro a makarantar masu bukata ta musamman dake Tudun Maliki a mazabar Guringawa dake karamar Hukumar Kumbotso ranar Larabar da ta gabata.

Exit mobile version