Kansila mai waklitar nazahabar Guringawa a karamar hukumar Kumbutso ta Jihar Kanoz Muslihu Ali ya nada matamaika har mutum 18. A cikin wasikar nadin, Kansilan ya ce mataimakan su 18 za su taimaka mishi ne wajen tafiyar da aikinshi yadda ya dace.
“Aikinsu shine su taimaka min, musamman wajen isar sa ayyuka don ci gaban al’ummata, shiyasa nake sanar da daukacin al’umma wanna nadin.” inji Muslihu
Wadanda aka nada din sune, Sulaiman Ibrahim Bako (PA), Yahaya Abdu a matsayin magatakarda, Kamalu Garba a matsayin mai bada shawara ta fannin watsa labarai, Usama Zubairu hadimin musamman a harkokin addini.
Da sauran mukamai, kamar, mataimakan musamman a taimakon-kai da kai, agajin jin-kai, kafofin sadarwa, harkokin siyasa da sauran mukamai.