Sharfaddeen Sidi Umar" />

Kansila Ya Rabawa Mata Teloli 20 A Sakkwato

Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Kansila a Jihar Sakkwato, Hon. Nasiru Abubakar ya dauki nauyin horas da matasan matan mazabarsa yadda ake sana’ar dinkin tela domin karfafa masu guiwa su zamo masu dogaro da kai.

Kansilan wanda ke wakiltar mazabar Sarkin Zamfara “B” da ke a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a Jam’iyyar APC ya kuma rarrabawa matan kyautar teloli a wajen bukin yaye su da aka gudanar a mazabar.

Daga cikin wadanda suka amfana da shirin na karfafawa akwai musakai da marasa galihu wadanda aka baiwa kudi da tufafi domin taimakawa rayuwar su.

Babban Jigon Dan Siyasa kuma babban mai tallafawa Jam’iyyar APC, Jarman Sakkwato, Alhaji Dakta Ummarun Kwabo A.A MFR ne ya albarkaci taron a matsayin Shugaban Taron wanda kuma ya jagoranci rarraba kayayyakin ga wadanda suka amfana.

A jawabinsa a wajen taron, Hon. Nasir Abubakar ya bayyana cewar ya bayar da tallafin ne domin cika daya daga cikin alkawulan da ya yi wa jama’arsa a lokacin yakin neman zabe.

Ya ce an samu nasarar bayar da tallafin ne a karkashin kungiyar bayar da tallafi wadda ba ta Gwamnati ba wadda ya kafa tun bayan zamansa wakilin al’umma wadda ke da sunan Shirin Bunkasa Rayuwar Matasa na Nasiru Abubakar (NAYEP)

Ya kara da cewar ya yi kokarin tara kudaden ne ta hanyar wasu kudade da kuma albashin da yake karba a kowane wata a matsayinsa na Kansilan da ke wakiltar mazabar.

A kan wannan Kansilan ya kalubalanci wadanda ke rike da mukaman siyasa da su dauki kyautata rayuwar al’ummar su da muhimmanci domin a cewarsa ba ya da dalilin rashin tallafawa al’ummarsa wadanda sune suka kai shi a matsayin da yake a yau.

“Babu dalilin da zai sa dan siyasa ya rika tunanin sai kawai a lokacin yakin neman zabe zai rika tunawa da jama’arsa. Albashi na ba wai kawai nawa ne ni kadai ba har da al’ummar da nake wakilta. Ina yin wannan ne domin in kalubalanci duk wanda zai gaje ni a wannan kujerar.” In ji shi.

A jawabinsa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato, Sulaiman Usman Danmadami ya yabawa Kansilan kan hangen nesa ta hanyar samar da romon mulkin Dimokuradiya ga al’ummar sa.

Ya ce Kansilan ya nuna yadda ya kamata shugaba ya kasance tare da alkawalin bayyanawa Gwamna Tambuwal hobbasar kwazon da Kansilan ya yi na taimakawa al’ummar mazabarsa.

“A tsayin shekaru biyar a matsayin Shugaban Jam’iyya ban taba ganin wani Kansila wanda ya yi irin wannan shiri na karfafawa jama’a ba. Ina tabbatar maka da cewar idan ka ci-gaba da irin haka to makomar ka za ta yi kyau domin a wata rana za a iya zaben ka a matsayin Gwamna.” Shugaban jam’iyyar ya bayyana.

A jawabinta na jin dadi, Asma’u Shehu ta bayyana farin cikin ta ga Kansilan kan wannan namijin kokarin da yayi na karfafa masu guiwa tare da rokon Allah ya ci-gaba da yi masa jagora.

Exit mobile version