Umar A Hunkuyi" />

Kanu Bai Aminta Da Hadaka Da Wani Dan Siyasa Don Yakar Buhari Ba –Kungiyar IPOB

Mataimakin shugaban kungiyar ‘yan asalin Biyafara, (IPOB), Uche Mefor, ya karyata rahotannin da ke cewa, shugaban kungiyar Nnandi Kanu, ya kulla wata yarjejeniya da wasu ‘yan siyasa domin yunkurin kawar da Shugaba Buhari, a lokacin babban zaben 2019.

Tsohon Ministan harkokin Jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ne a cikin wani rahoto da aka fitar daga gare shi ya ce, Kanu ya sha alwashin yin aiki tare da shi domin kawar da shugaba Buhari a babban zaben kasar nan na 2019, a lokacin da suka yi magana da shi ta wayar tarho a ranar ta Asabar.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Mefor, ya ce wannan magana da Fani-Kayode ya yi wata mummunar dubara ce ta bata sunan shugaban kungiyar na su ta IPOB.

Mefor ya ce, Kanu yana aiki ne domin dawo da martabar Biafara, ba gudu ba ja da baya a kan wannan kudurin na shi.

“Muna son mu yi amfani da wannan daman mu bayyana a sarari cewa, ba wani lokacin da Kanu suka kulla yarjejeniya da duk wani dan siyasa domin shiga cikin siyasar Nijeriya.

“Daga yanzun duk wata sanarwa da za a ji wacce ba daga bakin shugaban namu, mataimakin sa ko shugaban wata Jiha ba da ta shafi kungiyar ta mu ta IPOB ko kuma Shugaban namu ba, to wannan sanarwar karya ce.

“A karshe, Nnamdi Kanu, yana murna da kuma yaba wa daidaiku da kungiyoyin da suka taimaka a lokacin da ya shiga gaiba, wacce ba ta gazawa ba ce.

“Muna kuma gayyatar ku da ku saurari jawabin da Nnamdi Kanu ya yi wa ‘ya’yan kungiyar na shi ta IPOB da ma duniya baki daya daga birnin Tel Abib, na kasar Isra’ila, a kan manufar gwagwarmayar da yake yi.

“Bayan sauraran wannan jawabin na shi ne kadai za ka iya baiwa kanka shawarar makomar duk karairayi da farfagandar da ake yadawa a kansa.”

Exit mobile version