Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Jagoran ’yan ta’addar yankin Biyafara, Mista Nnamdi Kanu, ya garzaya kotu, domin kalubalantar ayyana su a matsayin ’yan ta’adda da wata kotu ta yi bad a jimawa ba.
A karar da ya shigar da yawun kungiyarsa ta IPOB mai fafutukar ballewa daga Nijeriya, Kanu ya ce, a bayyane ta ke cewa, hukuncin da waccan kotun ta Abuja ta yanke a ranar 20 da satumba, 2017, ta na mai ayyana kungiyarsa a matsayin ta ’yan ta’adda, kamar yadda rundunar sojin Nijeriya ta fara ayyana su, ba karamin kuskure ba ne, kuma a cewarsa ba daidai ba ne a haramta ayyukan kungiyar tasa.
Kanu ya kara da cewa, IPOB ba kungiya ce mai tayar da kayar baya ko kawo hautsini ba, illa dai kawai ta na kokarin nema wa yankinta ’yanci ne ba tare da saba wa kundin tsarin mulkin kasa ba, domin a matsayinsu na ’yan Nijeriya su na da ’yancin yin hakan matukar ba su shiga hakkin wani ba.
Kungiyar ta ce, wannan hukunci an yi shi ne kawai domin a dadadawa makiyansu, kamar sojojin da su kai wa Kanu farmaki a gidansa da ke yankin kwanakin baya.
Idan dai za a iya tunawa rundunar sojan Nijeriya ce ta fara kiran IPOB da sunan ’yan ta’adda bayan da ta zargi kungiyar da tunzura mutanenta su ka fara afka wa Hausawa mazauna yankin Kudu maso Gabas a kwanakin baya.
Hakan ya janyo martini daga wasu sassa, inda shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Bukola Saraki, ya soki lamirin rundunar sojan bisa afkawa gidan Kanu da sauran masu yunkurin ta’addanci a kan Hausawan.
Sai dai kuma hakan ya janyo wa Saraki suka daga sassa daban-daban na kasar, inda hatta lauyoyi da sauran masana shari’a ke ganin cewa, matakin na rundunar sojan kasar shi ne ya fi dacewa, an kafa rundunar ne domin ta kare Nijeriya daga dukkan wata barazana, ciki kuwa har da yunkurin keta kasar ko ballewa daga cikinta.
Kana masu wannan ra’ayin na ganin baiken Saraki da ya ke cewa, kamata ya yi a je kotu kafin a dauki matakin karfi ta hanyar hana su kasha Hausawan, inda ke sukar Saraki da ya manta da cewa, a lokacin da rikici ya balle za a iya rayuwa da yawan gaske, kafin kotu ta yanke hukunci. Don haka zuwa a dauki matakin gaggawa ya fi dacewa matuka gaya, in ji masu ra’ayin.