Ibrahim Muhammad" />

KAPAG Ta Bayyana Jin Dadinta Bisa Tarba Da Aka Yi Wa Gwamna Ganduje

Kungiyar KAFAG da Hajiya Balaraba Ibrahim tsohuwar mai baiwa Gwamnan Kano shawara akan ma’adinai ke jagoranta ta bayyana matukar farin cikinta bisa gagarumar tarba da kanawa suka fito suka yiwa Gwamnan Kano Ganduje da taya shi murnar nasarar da ya yi a kotu.

Ta ce, wannan tarba shi ne abinda Bahaushe ke cewa an kashe bakin tsanya. Abinda yan hamayya ke ce ba’a son Ganduje an karyatasu duk mutane da suka fito wannan tarye ba kudi aka basu ba soyayyace tasa.

Hajiya Balataba Ibrahim ta kara da cewa wannan ya nuna cewa mai hirma Gwamna Ganduje mai gaskiya ne.Allah yana tare dashi kuma al”ummar Kano suna goyon bayansa. Don wannan da bazata manta dashi ba. Musamman a matsayinta ta wacce ta baro wani gida na siyasa ta dawo wajen Gwamna Ganduje ta bada goyon baya ya sake samun nasara a zabe.

Ta kara da bayyana godiyarta ga Allah da rokon Allah ya bai wa Gwamna ikon sauke nauyi ya fitar dashi kunyar makiya yayi mulki lafiya al’ummar Kano su cigaba da morar ayyula fiye da wanda ya yi a baya.

Balaraba ta ce, mai girma Gwamna mutunne mai kyakyawar mu’amala yasan darajar mutane. Muna fata al’umma za su cigaba da  bada hadin-kai da yiwa Gwamna addu’a ya samu ya cigaba da ayyukan alkhairi a Kano.

Hajiya Balaraba ta ce, a shirye sule su baiwa Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje hadin-kai da goyon baya dazai kai ga nasara.

Exit mobile version