Sanusi Chen" />

Kar Kasar Amurka Ta Dinga Nuna Damuwa Yayin Da Take Hulda Da Kasar Sin

Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya yi wani jawabi a kwanan baya, inda ya yi suka kan kasar Sin, yana mai cewa, wai “wasu hukumomi masu kula da aikin tsaro na kasar Sin suna kokarin satar fasahohin kasar Amurka, har da fasahohin aikin soja mafi ci gaba na kasar”. A sa’i daya, kafar yada labaru ta kasar Amurka Bloomberg News, ta watsa wani labarin cewa, kasar Sin ta saka na’urorin satan bayanai a wasu kamfanoni masu fasahohin zamani na kasar Amurka, labarin da wadannan kamfanoni da ma’aikatar tsaron kasar Amurka suka karyata shi. Duk da haka, kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun kare kansu da cewa, wai “ko da yake kasar Sin ba ta yi illa ga tsarin samar da kayayyakin latironi ga kasuwannin kasar Amurka ba tukuna, amma a nan gaba za ta yi.” Wannan magana tamkar jita-jita ce, wanda kuma hakan ya nuna irin damuwar da ake ji a zukatan wasu ‘yan Amurka, dangane da huldar dake tsakanin kasarsu da kasar Sin.
Yanzu fasahohi masu alaka da yanar gizo ta Internet sun samu ci gaba sosai, abin da ya sanya jama’ar kasashe daban daban samun sauki a zaman rayuwarsu. Sai dai ba su fahimci fasahohi da na’urori masu alaka da yanar gizo ba. Idan har aka ambaci aikin “leken asiri”, za a kara samun damar yaudarar jama’a sosai. Wannan yanayi ya sa a kan samu jita-jita wai wani na kulla wata makarkashiya.
Ga misali, yayin babban zaben kasar Amurka na shekarar 2016, an samu labarai na karya da yawa a shafunan sada zumunta, musamman ma masu alaka da ‘yar takara Hilary Clinton. Wani daga cikin labaran ya ce, an yi amfani da wani wurin sayar da abinci na Pizza, wajen fataucin yara da kuma cin zarafinsu. Wannan labari na karya ya sa wani Ba’amurke ya dauki bindiga don kai hari ga wannan wurin sayar da abinci… A waccan lokaci, kusan ba a lura da hakikanin abun da ya faru ba, inda ake mai da hankali kan ra’ayi na wasu mutane daidaiku kawai.
A halin yanzu, muna ganin cewa, duk da cewa wasu kamfanonin fasahohin zamani, ciki har da Apple da Amazon gami da ma’aikatar tsaron kasar Amurka, sun karyata rahotannin da kamfanin watsa labarai na Bloomberg na Amurka ya ruwaito na cewa, wai kasar Sin ta saka “na’urar satar bayanai” a kwamfuta, amma kamfanin Bloomberg ya ci gaba da wallafa irin wadannan bayanai don shafawa kasar Sin kashin kaji, al’amarin da ya jawo raguwar darajar hannayen jari ta fuskar kimiyya da fasaha a duk fadin duniya.
Amma karya dai karya ce, kuma maimaita ta, ba zai sa ta zama gaskiya ba. A kwanakin baya, shahararren masanin harkokin kasa da kasa na Amurka, wanda ake kiransa “masanin kasar Sin”, dokta Robert Kuhn, ya bayyana a wajen shawarwari tsakanin masana harkokin Sin da Amurka a jami’ar Harvard dake Amurka cewa, idan aka gano wata kasa ta saka na’urar satar bayanai a cikin kwanfuta, domin tona asirin wasu kananan kamfanoni kalilan, wannan kasa za ta yi babbar hasara wajen yin cinikayya. Babu shakka, babu wata kasa wadda za ta yanke irin wannan shawara ta rashin hankali.
Hakika, ya kamata mu yi tunani mai zurfi, da bin gaskiya yayin da muke kara fahimtar sabanin ra’ayi, da matsalolin dake cikin dangantakar Sin da Amurka.
Muna iya ganin cewa, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, kafofin watsa labaran Amurka suna kirkiro labarai da rahotannin dake cewa, wai kasar Sin na saka “na’urar satar bayanai”, makasudinsu shi ne, gabatar da shaidu ga gwamnatin Amurka, wajen tsara sabbin manufofinta kan kasar Sin. Amma irin wadannan shaidu marasa gaskiya, za su kara raunata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, wadda a yanzu haka ke fuskantar kalubale da dama. Babban manazarci a cibiyar harkokin Asiya ta jami’ar Harvard ta Amurka dokta William H. Overholt, ya taba bayyana cewa, kila masu nuna ra’ayin kabilanci na Amurka, ciki har da ‘yan siyasa da dama, za su yi amfani da zargin da ake wa kasar Sin, na cewa wai tana satar bayanan sirri don hura wutar rikici, musamman a daidai wannan lokaci, wato yayin da ake fuskantar abubuwa na rashin sanin tabbas da dama a dangantakar Sin da Amurka, kana za su kara ingiza bukatar gwamnatin Amurka ta sauya manufofinta kan kasar Sin, da rage dogaronta kan Sin.
A hakika dai, tun daga bana, dukkan matakan da kasar Amurka ta dauka sun nuna rashin hankali, da kuma rashin tushe na kasar wajen gudanar da harkokinta, kamar “Daftarin ba da izinin tsaron kasa” da ta fidda, wanda ya shafi batun Taiwan na kasar Sin, da kuma hana ayyukan zuba jarin da kamfanonin kasar Sin suka yi a kasar Amurka, da kuma “yarjejeniyar USMCA” da aka kulla tsakanin kasashen Amurka, da Canada da kuma Mexico, inda suka tsara sharadin rashin adalci kan kasashen dake karkashin tsarin gurguzu.
Haka kuma, bisa rahoton da aka samu daga kasuwar yawon shakatawa a tsakanin kasa da kasa ta kasar Amurka, an ce, adadin kudin da mutanen kasar Sin suka kashe a kasar Amurka a shekarar 2017, ya kai matsayin farko cikin mutanen ketare da suka je yawon shakatawa a kasar. Amma cikin hutun bikin ranar kafuwar kasar ta Sin na kwanaki 7 na shekarar bana, adadin mutanen da suka je yawo a kasar Amurka ya ragu sosai, dukkanmu mun san dalilin da ya haddasa wannan raguwa.
Cikin jawabinsa, Mike Pence ya ruwaito maganar Lu Xun, babban marubucin kasar Sin, domin bayyana ra’ayinsa cewar, kasar Sin ta nuna rashin adalci kan harkokin sauran kasashen duniya. Amma, a hakika dai, maganar ta malam Lu Xun ta fi dacewa da hali na gwamnatin kasar Amurka. Watau yadda kasar Amurka take ganin ci gaban kasar Sin ba ya kan tsari na aldaci, kuma ba ta daidaita huldar dake tsakaninta da Sin yadda ya kamata ba, lamarin da ya sa, muka rasa wasu kyawawan damammaki wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, yayin da kuma hakan ya haifar da matsaloli ga kasashen duniya a fannoni da dama. (Masu fassarawa: Bello Wang, Murtala Zhang, Maryam Yang, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version