Kar A Siyasantar Da Kashe-kashen Makiyaya –Osinbajo

Daga Umar A Hunkuyi

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya gargadi ‘Yan Nijeriya da kada su Siyasantar da rigingimun da ake samu na makiyaya a wannan lokutan, a cewarsa, hakan zai iya kunna wata wutar fitinar ta daban da za ta iya shafar dukkanin kasarnan. Mataimakin Shugaban Kasan wanda yake tare da wasu Ministoci, wasu Wakilan Majalisoshin kasa da kuma Kwamandojin askarawan kasarnan, a wajen addu’o’in wannan shekarar na tunawa da ‘Yan mazan jiya a Cbiyar Kiristoci ta kasa da ke Abuja.

Osinbajo, ya ce, yana yin wannan gargadin ne, a bisa la’akari da yadda sanya Siyasa a lamarin rikicin Boko Haram tun a farkon lamarinsu ya yi sanadiyyar habaka tarzomar na su, yana mai gargadin ‘Yan Nijeriya da kada su kuskura su sake maimaita shigen wancan kuskuren.

“Ya wajaba mu san cewa, kamar yadda wadannan makasan suke aiwatar da kashe-kashen rashin Imani, to hakanan kuma sanya siyasa a cikin maganar shima yana da na shi hadarin, kamar dai Karin maganar nan ce, wacce ke cewa, ‘Kashe wutar da ke ci balbal, ta hanyar watsa mata Fetur, tamkar kara ruruta ta ne’

“Tilas mu gujewa sanya siyasa a cikin wannan barnar. Daya daga cikin dalilan da suka sanya aka dauki tsawon shekaru ana fama da ta’addancin Boko Haram, shine sanya siyasa a cikin wannan ta’addancin, akwai wadanda suke nufin su yi amfani da wannan rigimar a siyasance.

“Yau ma ga shi muna ganin wadanda suke son cimma wani buri nasu na siyasa ta hanyar kashe Mata da Yara kanana a Adamawa, Benuwe, Jos da sauran wasu wuraren masu yawa, ta hanyar jefa kalaman kabilanci da na bambancin Addini.”

“Don haka ya hau kanmu bakidaya da mu bi duk hanyoyin da suka dace wajen hana su yin amfani da gaba na siyasa, wanda hakan zai iya zama barazana a kan hadin kanmu da kuma zaman kasarmu lafiya. Kamar yadda za mu ci gaba da yin fafutukar samar da zaman lafiya a dukkanin wuraren da ake fama da wadannan fitintunu.

“Na kuma yi alfahari da kasancewata a wannan wajen, domin na shiga cikin iyalai da abokanai wajen jinjinawa Jarumawanmu da suka kwanta dama, ta hanyar sadaukar da kawukansu. Duk Jarumi Namiji ko Macen da aka kashe a fagen daga, daman can ya rigaya ya aminta da ya sadaukar da ransa ne wajen ganin tabbatuwar wannan kasa tamu.

“Da yawa sun mutu a wasu hanyoyi masu ban tsoro, da yawa sun tafi sun bar ababen kaunarsu na daga iyalai da suka hada da Matayensu, Mazajensu, ‘Ya’yayensu, Jikokinsu da kuma iyayensu.”

“A shekarun baya mun shaidi ayyukan ta’addanci da rashin Imani daga ayyukan ‘Yan ta’adda masu tsatsauran ra’ayin Boko Haram, a Arewa maso gabashin kasarnan, mun kuma ga yadda jajrtattun Sojinmu, ‘Yan Sandanmu, kai hatta ma fararen hularmu suka tashi haikan ta hanyar hada kai wajen fatattakan wadannan makiyan, suka kuma maido da zaman lafiya a da yawa daga cikin wadannan wuraren.

“A kwannan nan kuma mun ga kashe-kashen da suka auku a dalilin farmakin makiyaya da kuma manoma da sauran al’ummu, mun kuma ga yadda wasu al’ummun da manoman ke ta farmakan makiyaya.”

Osinbajo, ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari, ganin yadda rikici da kuma salwantar rayuka  ya rika afkuwa a Jihohin Ribas, da kuma kashe-kashen Badoo, a Jihohin Legas da Ogun, nan take sai ya umurci ‘yan Sanda da kuma Sojoji da su hanzarta daukan matakin gaggawan da ya dace domin murkushe rigingimun, da kuma tabbatar da sun kama masu haddasa su an kuma hukunta su.

“Shugaban Kasa kuma, a kullum yana cikin tattaunawa da hukumomin tsaron da suka dace wajen ganin an shawo kan dukkanin lamurran,” in ji Osinbajo.

Ana shi wa’azin, Bishop na yankin Jos, Bishop Benjamin Kwashi, cewa ya yi, “Duk mun taru a wannan wajen domin mu yi maku godiya a kan aikin da ku ke yi mana, muna kuma alfahari da ku. Muna kara yi maku godiya a kan aikin da ku ke yi wa wannan kasa tamu.

“Sojoji sune fatan wannan kasar, suna aiki ne ta hanyar sadaukar mana da rayukansu, wajen yakan ‘yan Boko Haram, yakan maharan makiyaya, yakan masu yin garkuwa da mutane da kuma dukkanin mugaye Maza da Matan da ba sa nufin wannan kasar na mu da alheri, da yawa daga cikinku sun mace tun kafin lokacin mutuwarsu ya yi.

“Lokuta da yawa idan na yi la’akari da yawan mutanan da wadannan mugayen ke kashewa, sai na rika tunanin, ko ta ya ya ne Shugabanninmu na siyasa ke iya yin barci, ni ban sani ba, saboda a matsayina na Limami, na halarci addu’o’in Jana’iza sama da addu’o’in Haihuwa da na aure a nan Jos.”

“Kananan yara ake ta kashewa, da kuma fakiran da kila waninsu ma har ya mutu ba zai taba mallakan Naira, 200,000, na shi ba. Mutanan da ba sa iya hassala komai, ba kuma za su iya cutar da kowa ba, sune ake ta kashewa. A sakamakon ayyukan wasu mabarnata da a kullum muke ta sakayawa a maimakin mu fadi gaskiya. Muna nan dai muna ta fatan alheri ga Sojojinmu, muna kuma da kyakyawan fatan Allah zai kawo mana mafita a kan wannan lamarin.

 

Exit mobile version