Hukumar ‘yan sandan Nijeriya ta kara wa ‘yan sanda 6,455 matsayi, Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya Idris Ibrahim ne ya mika sunayen ‘yan sandan.
A sanarwar da mai magana da yawon hukumar, Mista Ikechukwu Ani ya fitar sabbin wanda aka kara wa matsayin sun hada da: Hilda Ibifuro-Harrison wacce ta zama mataimakiyar Sufeto-Janar, mataimakan kwamishinan ‘yan sanda, Ajani Olasupo Babatunde, da Olukola Taira Shina, su kuma sun koma matsayin kwamishinonin ‘yan sanda.
Sufritanda ‘yan sanda 47 ne suka zama manyan Sufritandan ‘yan sanda, sannan mataimakan Sufritanda su 498 ne suka samu mukamin Sufritandan ‘yan sanda.
Sufetoci 5,907 kuwa sun zama mataimakan Sufritanda, a yayin da Mohimi D. Idgal da Aji Ali Janga suka yi gaba daga mukamin mataimakan kwamishinan ‘yan sanda zuwa matsayin kwamishinonin ‘yan sanda na rikon kwarya.