Daga Ibrahim Muhammad,
Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa, Hon. Mahe Garba Garun Danga ya bayyana cewa Karamar Hukumar tasa tamkar gida ne ga jam’iyyarsu ta APC domin duk zabubbukan da aka yi a baya, babu wata kujera da jam’yyar ba ta yi nasara a kai ba.
Ya ce, saboda haka ma aikin sabunta rijistar jam’iyyar da ake yi, mutanen Karamar Hukumar Gabasawa suna tururuwan zuwa suna sabunta katin, duk da an dan sami akasi da katunan Karamar Hukumar ba su zo da wuri ba, amma yanzu da aka karbo ana yi, kuma jama’a nata zuwa suna karba.
Shugaban na Gabasawa ya yi kira ga jama’ar, Karamar Hukumar su ci gaba da ba su hadin kai domin duk abubuwa da suka yi a baya da nasarori da suka samu ba kokarinsu ko dabarar su ba ne Allah ne ya ba su iko suka aiwatar da abubuwa na ayyukan ci gaba bisa irin hadin kai da jama’a suka ba su, kuma cikin yardar Allah za su ci gaba da dorawa akai daga inda suka tsaya ta hanyoyi daban-daban na taimaka wa al’umma.
Ya yaba wa dan majalisarsu ta tarayya mai wakiltar Gabasawa da Gezawa, Hon. Nasiru Abdu Gabasawa bisa yadda yake taimaka wa ci gaban al’umma, ya yaba da irin tallafin da ya baiwa iyayen kasa Dagatai da Limamai da dalibai irin wannan ake bukata kawo hanyoyi da za a rika taimaka wa jama’a.
Hon. Mahe Garba Garun Danga ya kara yaba wa dan majalisar tarayyan da irin wannan gagarumar gudumawa da ya kawo, dama a tsarin dan majalisar ba wani wata da zai zo ba tare da ya aiko da kudi na tallafa wa jama’a daban-daban ba, mazaba-mazaba ana tallafa wa al’umma, wanda ba ma bayyanawa ake ba, sai dai su da suka sani.
Ya ce, yanayi Irin wannan na tara jama’a a tallafa musu a bayyane yanzu ya fara, amma gudumawa da yake baiwa jama’a aikin sa ne a kowane lokaci.
Hon. Mahe Garba Garun Danga ya yi kira ga al’ummar Kano su ci gaba da baiwa manufofin Gwamnatin Kano, karkashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje goyon baya don ci gaba da ayyukan alkhairi da ake gudanarwa.