Connect with us

RIGAR 'YANCI

Karamar Hukumar Giwa Za Ta Feshe Gurare Sama Da 300

Published

on

A ranar satin makon daya gabata ne shugaban karamar hukumar Giwa dake jihar kaduna honorabul Abubakar Shehu Lawal Giwa ya kaddamar da Feshin magani riga karin korona Bairon a karamar hukumar.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada  labarai da suka shaida da kaddamar da Feshin a karamar hukumar kuma ya aiko mana da rahotosa kamar haka.

Taron an gudanar da shine a harabar sakateriyar ta karamar hukumar Giwa dake garin Giwan

Sarakuna da masu anguwanni ne da daraftocin mulki na karamar hukumar da jami’an tsaro  da wakilan kungiyoyi ne suka kasance a wajan kaddsmar da feshin

Mataimakin Shugaban karamar hukumar ta Giwa honorabul Lawal Ibrahim,Manti ya fara gabatar da jawabin bude taro tare da yin maraba da manyan bakin da suka Sami halattar taron.

Shi ma sakataren karamar hukumar ta Giwa Alhaji Usman Isma’i Giwa yayi jawabi inda ya tabbatar da cewa karamar hukumar Giwa ta shirya Tsafe don gudanar da feshin maganin rigakafin Koraona Bairos da sauran cutuka a gurare masu muhimmanci har guda kusan 300.

Karshe sakataren ya nuna gofiyarsa ga shugan karamar hukumar ta Giwa bisa kokarin sa a bangaren kula da jamar karamar hukumar ta Giwan yace Allah yasa yadda aka fara lafiya Allah ya sa a gama  lafiya.

Shi ma hakimin Kasar Giwa Alhaji Alhaji Abdul-Kareem Aminu (Wanban Zazzau) a nasa jawabin yayi godiya ne ga Shugaban karamar hukumar ta Giwa bisa kokarinsa, kuma ya yabawa gwnan jihar Kaduna Malam Ahmed Nasiru El-Rufai bisa kokarin da yake yi da kawo hanyoyin dakile wannan cutar mai matukar barna ga rayuwar bil-Adama Kuma ya yabawa mai martaba sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris CFR bisa tarbiya da Jan hakali da yake wa Jama’ar kasarsa don samun zaman lafiya mai dorewa yayi fatan yadda a ka fara lafiya Allah yasa a gama lafiya.

Malam Yunusa Muhammad Abdullahi shene shugaban kamfanin Yam enbironmental health consulting  and debices kuma she ke lura da yadda feshin zai gufan a yayi yakewa manema labarai jawabi ya tabbatar da cewa kamfanin zai bi dukkan ka’idojin da karamar hukumar ta bashi yayin gudanar da feshin.

Kuma ya yi karin haske akan yadda feshin zai gudana da cewa, feshin zai amfanar da duk inda a ka yi s hi har tsawon wata hudu. Kuma dole a kauracewa duk Inda a ka yi zuwa kwanaki hudu, kuma baya ga rigakafin cutar korana Bairos da yakeyi akwai maganin sauro don kaucewa annobar cizon sauro don hakan ya nemi jama’ar karamar hukumar ta Giwa dasu Basu hadin kai yayin da suke gudanar da aikinsu kuma yayi fatan alheri ga jama’ar garin Giwan baki daya.

Karshe Shugaban karamar hukumar ta Giwa ne yayi jawabin kammala taron tare da mika godiya ga mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed Nasiru El-Rufai bisa kokarin sa na dukkannin aiyukan da yake gabatarwa a fadin jihar ta Kaduna.

Shugaban ya tabbatar da cewa za a feshe gurare fiye da 300 muhimmai a karamar kilumar ciki akwai kamar asibitoci da makarantu da ofishin ‘yan sanda da kasuwanni da makarantu Kuma ya nemi hadin kan jama’a yayin gudanar da aikin feshin .

Ya zuwa hada wannan labarin har an feshe makarantar Mata ta Gwamnati dake garin Giwa (GGSS GIWA)
Advertisement

labarai