Karamar Hukumar Jibia Ta Raba Kayan Kariya Bayan Bullar Korona

Karamar hukumar Jibia ta raba kayayyakin kariya daga kamuwa da cutar corona birus a yankin.
Kayayyakin an rabasu ga masallatan juma’a, coci-coci, sakatariyar karamar hukumar, ofisoshin jami’an tsaro, tashoshin mota, kananan yankoki, kasuwanni da kuma wuraren gundumomin hakimi guda biyu, da kuma dagattai.
Da ya ke raba kayayyakin kariyar, shugaban sashen mulki na karamr hukumar ta Jibia Alhaji Sada Ahmad Dandagoro ya hori wadanda suka amfana da suyi kyakkyawan amfani da tallafin.
Daraktan sashen kula da ma’aikata Malam Bilya Musa, da Alhaji Sada Ahmad sun gargadi mutane da cewa corona birus cuta ce mai kisa, inda ya bukace su da su rungumi matakan kariya daga kamuwa da cutar.
Da ya ke magana Daraktan samar da ruwa da tsaftar muhalli na Jibia ya Zayyana Batagarawa ya shawarci al’umma dasu rungumi dabi’ar tsabta, sannan kuma su kai rahoton duk wani mutum da suke zargi ga hukumomin lafiya.
Kayayyaki da aka raba sun hada da, sinadarin wanke hannu, sabulu na ruwa, takunkumin rufe fuska, bokitai da safar hannu da dai sauransu.
Haka zalika karamar hukumar Jibia ta raba kwafi-kwafi na littattafan al-kur’ani mai tsarki ga al’ummomi da limamai na gundumomin hakimai biyu na yankin.
Shugaban sashen mulki na karamar hukumar Alhaji Sada Ahmad Dandagoro wanda ya samu wakilcin Daraktan Kula da walwalar ma’aikata Bilya Musa Mani. Tallafin na da nufin karfafa gwuiwar karatun al-kur’ani a cikin watan Ramadan.
Da ya ke magana a madadin limaman guda biyu Sarkin Malaman Jibia Malam Ibrahim Sabi’u yayi nuni da cewa karatun al-kur’ani yana kawo zaman lafiya da hadin kai a cikin al’umma.
Sarkin Arewacin Katsina Hakimin Jibia Alhaji Rabe Rabi’u wanda ya samu wakilcin sakataraneshi ya godema karamar hukumar dangane da tallafin da ta bayar.

Exit mobile version