Connect with us

LABARAI

Karamar Hukumar Katagum Ta Himmatu Wajen Inganta Rayuwar Jama’a – Mohammed Hassan Karamar Hukumar Katagum Ta Himmatu Wajen Inganta Rayuwar Jama’a – Mohammed Hassan

Published

on

Me ka sanya a gaba wajen jagorancin karamar hukumar Katagum musamman game da shirin yaki da shara da sauro?

Daga lokakacin da na kama wannan jagoranci niyyata shi ne naga cewa na kyautata don sauke nauyin da aka dora min don na fita hakkin duk wani mutum da hakkinsa ke wuyana musamman a fannin inganta lafiya, saboda a baya mun samu rashin mutane da yawa sakamakon zazzabin cizon sauro, don haka cikin karamin lokaci ba yabon kaiba kowa ya san mun yi kokari wajen inganta lafiyar mutanen mu.

Bayan haka kowa ya san garin Azare akwai shara ta mamaye ko’ina don haka na dauko hayar motocin kwashe shara muka kwashe sama da tirif dubu da dari biyar a cikin Azare sauran yankuna kuma kusan tifa dubu , mutane sun amfana wajen shiga harkar kwashe sharar, gari ya zamo ana ta hayaniyar tsabtace shi masu tifofi suka samu aiki cikin sauki. Bayan haka kuma na sayo kayan feshin sauro aka horas da ma’aikata muka shiga aikin yakar sauro muna kuma ci gaba da wannan aiki kowane wata don samar da lafiya ga mutanenmu.

A fannin aikin ruwa mun gyara rijiyoyin burtsatse a kalla guda 130 da famfuna a gundumomi 20 da ake da su da kuma tona sabbin rijiyoyi don samun ruwan sha mai tsabta saboda lafiya ta inganta. A takaice lokacin da nazo kowane shugaban karamar hukuma na jihar Bauchi ya sayi mota a kalla ta milyan biyu don amfanin ofishinsa, amma ni naga yin hakan zai kashe kudi da yawa sai na dauki tsohuwar motar shugaban karamar hukuma na gyarata kan kudin da bai wuce Naira dubu dari huduba, sauran kudin sai na gyara motar mataimakina da wasu motoci har aka samu rarar kudi aka yi wasu ayyuka da su.

 

Wane kokari ka yi wajen inganta hanyar samun kudi a wannan yanki don gudanar da ayyukan raya kasa?

Akwai tiken shanu wanda yana cikin hanyar samun kudin shigarmu. Don haka muka yi wajen zaunar da mutane idan sun gama cin kasuwa da wajen ajiye shanu da wajen samar da ruwan shan su da wajen lodin shanu a kasuwar dabbobi don samun kudin shiga kowa ya je wajen zai gani.

A Madara an duba irin matsalar wutar lantarki da suke da ita za mu bayar da aikin gyara wutar da ta lalace wajen shekaru biyu. Mun gyara shagunan kananan hukumomi da aka lalata a baya mun gina kwalbatoci a kasuwar Azare tare da haskaka titinan garin da kuma raba filayen a kalla 700 don mutane su gina gidaje su tsuguna.

 

Game da batun hanya da ilmi kuma ko akwai abin da ka aiwatar?

Hakika an gudanar da ayyuka musamman mutanen garin gambaki da suke bukatar hanya shekaru da dama sun zo sun mana kuka game da lalacewar hanyarsu tuni za mu fara aikin, saboda idan damina tazo suna samun wahala sosai. Bayan haka akwai hanyoyi da dama da muka bayar da aikin gyarasu a yankunan mu. Akwai kuma wani shiri na inganta lafiyar mata masu juna da kananan yara da muka fito da shi nan bada jimawaba za mu fara tallafa musu. Don haka muna neman addu’ar mutanen wannan yanki don Allah ya kawo mana zaman lafiya, muna son kowa ya tashi da addu’ah don a samu kwanciyar hankali daga bala’in harin da ya samemu shekarun baya, don haka muna rokon Allah ya kare wannan yankin ya tona asirin masu tayar da hankalin mutane.

Kuma ina rokon jama’a idan lokacin sanya yara makaranta ya zo don Allah kowa ya kai yaransa don muhimmancin da karatun zamani ke da shi ya kamata iyaye su waye su samawa yaransu rayuwa mai inganci. Ta hanyar karatu ake taka duk wani mataki na ingancin rayuwa a wannan zamani. Duk abin da mukace zamuyi mutane su fahimcemu muna yine don ci gaban su, kuma muna neman hadin kan jama’a game da duk wani abin da ya shiga musu duhu, da fatar Allah ya bamu ikon sauke nauyin da aka dora mana, kuma muna marhabin da shawarar kowane mutum matukar don amfani da ci gaban jama’a da yankin ne.

 

Daga karshe menene nasihar ka ga mutanen Katagum da Jihar Bauchi?

Ina jan hankalin mutane su fahimci zaman lafiya shine gaba da komai don haka a zauna da juna lafiya a yi harkokin siyasa lafiya, bayan haka a taimaki wanda basu da shi don a zauna lafiya. A kuma kaurace wa taka doka don a samu gina kasa a samu ci gaba mai amfani da fata za a ci gaba da addu’a Allah ya bamu zaman lafiya da ci gaba mai amfani, Allah ya taimaki shugabannin mu ya basu ikon sauke nauyin da aka dora musu don a gina kasa kowa ya rayu cikin walwala da ci gaba mai amfani.
Advertisement

labarai