Sagir Abubakar" />

Karamar Hukumar Kurfi Ta Raba Buhunnan Gero Ga Mabukata

Majalisar karamar hukumar Kurfi ta bayar da gudummuwar buhunnan gero da na masara ga ‘yan gudun hijira sama da dari daga garuruwan Kasai da Wagini da Hambama da ke cikin yankin karamar hukumar Batsari wadanda aka ba matsugunni a cikin garin Kurfi.

Shugaban kwamitin rikon karamar hukumar Alhaji Jabiru Abdullahi Tsauri ya bayyana gudummuwar lokacin da ya kai masu ziyarar jaje dangane da harin da ‘yan bindiga suka kai masu.

Ya yi kira ga masu hali da su kai ma mutanen dauki don saukaka masu wasu matsalolin da suke fama da su a sansanin.

Alhaji Jabiru Abdullahi ya bayar da tabbacin cewa majalisar karamar hukumar zata cigaba da bayar da dukkan taimakon da ya dau ga ‘yan gudun hijira.

Exit mobile version