Sagir Abubakar" />

Karamar Hukumar Musawa Ta Raba Magunguna

Majalisar karamar hukumar Musawa ta rarraba magunguna daban-daban na kimanin miliyoyin nairori ga kanan asibitoci goma a yankin.

Da yake jawabin a wajen rabon kayan shugaban kwamitin rikon karamar hukumar Dr. Habibu Abdulkadir yace za a bai wa na rasa lafiya magungunan kyauta.

Dr. Habibu Abdulkadir ya umurci sashen kula da lafiya da ya tabbatar cewa ba a karkatar da ko kwaya daya na maganin ba, domin kuwa za a dauki matakin ladabtarwa ga wanda ya saba umurnin.

Ya bayyana cewa sauran cibiyoyin kiwon lafiya za su amfana da wani kason magungunan da karamar hukumar za ta samar.

Dr. Habibu Abdulkadir ya yi nuni da cewa gwamnatin jiha ce da hadin guiwar karamar hukumar Musawa suka tallafa domin taimakawa wadanda abun ya shafa daga ciki harma da ‘yan gudun hijira da marayu da sauran mabukata a cikin yankin karamar hukumar.

Exit mobile version