Karamar Sallah: Babban Limamin Bauchi Ya Nemi A Rage Farashin Kujerar Hajji

 A Talatar nan ne miliyoyin musulmai a jihar Bauchi suka yi ta fitowa kansu da kwarkwatansu domin gabatar da sallah mai raka’a biyu ta Idul Fitr bayan da suka kammala azumtar watan Ramadan. Jim kadan bayan kammalawa an yi addu’ar ci gaban kasa da kuma jihar Bauchi.

 A bisa al’ada, babban Limamin gari shi ne ke jagorantar miliyoyin jama’a wannan sallar da kuma gabatar da huduba mai ma’ana. A gefe guda kuma iyayen kasa Hakima, shugabanni sukan zama daga cikin mahalarta sallahr. A Bauchin dai, Mai Martaba Sarkin na Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman, da gwamnan Bauchi, Sanata Bala A. Muhammad sun kasance daga cikin miliyoyin jama’an da suka halarci wannan sallar a babban filin Idi na Bauchi.Da yake jawabinsa a filin Idi a yayin gudanar da Sallar Idin, babban Limamin Bauchi, Bala Ahmed Baban-Inna ya bukaci shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da ya taimaka wajen dubiya kan tsadar farashin kudin kujerar aikin hajji, yana mai shaida cewar rage farashin ne zai baiwa talawa damar sauke Farali.

Imam Baban-Inna ya shaida cewar farashin kudin kujerar Hajji ya yi matukar yawa wanda jama’a da daman gaske ba su iya samun zarafin biya domin zuwa ga sauke farali, yana mai neman shugabanni da su tashi tsaye wajen kira ga rage kudin da samar da sassauci a wannan bigiren.

“Ina mai rokon shugaban kasa Buhari da ya duba ya yi la’akari da tsadar kudin kujerar aikin hajji da hukumar jin dadin alhazai take amsa a hanun masu niyyar zuwa aikin hajji domin sauke farali. kudin ya yi yawa gaya,” A cewar Limamin.

Wakilinmu ya shaido cewar yanzu haka kudin kujerar aikin hajji ya zarce naira miliyan N1.5 ga kowani Alhaji, wanda hakan ke kara tilasta ma wasu rashin samun damar biyan kudin domin sauke farali.

Alhaji Bala Ahmed Baban-Inna a gefe guda kuma ya yi kira ga masu hanu da kumbar susa da suke taimaka wa marayu da marasa karfi da suke cikin al’umma domin rayuwarsu su ma take inganta, kana ya kuma bukaci jama’a da suke sauke Zakka da kuma Zakkatul Fitr domin dacewa da dumbin ladar da ke cikin hakan.

Har-ila-yau, ya kuma tsawatar kan aikata munanan dabi’u da suka shafi madugi, zinace-zinace, luwadi da sauran munanan alkaba’in da suke janyo wa kasa munanan bala’i, ya hori jama’a kan suke kaurace wa munanan dabi’un domin kauce wa saba wa Allah.

Daga nan ya jinjina wa gwamnan Bauchi, da Sarkin Bauchi a bisa fadakarwar da suka yi ta yi a lokacin zaben 2019 wanda ya sanya aka yi zaben lafiya, kana ya kuma yi fatan nasara a bisa kammala azumin watan ramadan lafiya, sai ya hori jama’a da suke ci gaba da dabba’a ababen da suka koya a cikin watan na Ramadan.

Babban Limamin ya nemi iyaye da suke kokarin sanya Ido sosai a kan rayuwar ‘ya’yansu domin daurasu a hanyoyin da suka da dace.

A ganawarsaa ‘yan jarida Sarkin Bauchi Alhaji (Dr) Rilwanu Sulaiman Adamu ya shaida cewar,  “Allah ya maimaita mana, ya kuma kara mana yalwa, lafiya da kwanciyar hankali. Allah ya maimaita mana ya sa zamu kai na badi,”

Daga bisani kuma Sarkin na Bauchi ya yi wa jama’arsa fatan alkairi da yi musu addu’a, “Muna wa Allah (T) godiya da ya nufashe muka yi Azumin watan ramadana lafiya har muka zo ga ranar Sallah.

“Mu na addu’ar wadanda suka rigayemu Allah ya jikansu, mu da muke raye muna addu’ar Allah ya kyautata karshenmu.

“Mu na godiya wa Malamai daga masallatai daban-daban a jihar Bauchi da ma kasa baki daya a bisa gudanar da tafsirai da fadakawar da suka yi ta yi, Allah ya sa abun da suka koyar ya amfane mu.

“Na farko mu yi ta fatan alkairi a tsakaninmu, mu ji tsoron Allah a dukkanin al’amuranmu, tsoron Allah shine ke haifar da komai na kwarai, idan kana tsoron Allah ba zaka aikata ta’addanci ba, idan kana tsoron Allah za ka yi adalci. Don haka muna rokon Allah ya sanya mana tsoronsa a dukkanin halayenmu,” a cewarshi.

Sarkin ya bukaci al’umma su kasance masu hakuri da juna, yana mai shaida cewar hakuri babbar guzurin samun nasarace a rayuwa, yana mai shaida cewar gaggawa aiki ne na shedan don haka ya nemi jama’a su kauce mata, kana ya nemi a yi wa shugabanni addu’a domin su samu nasarar kyautata kasa da ci gaban kasa, “Mu yi wa shugabanni addu’a Allah basu ikon yin abun da ya dace, mu kuma mu yi ta hakuri har zuwa lokacin da Allah ya sa bukatunmu za su biya,” A cewar shi.

Ya yi fatan a kammala bukukuwan sallah lafiya, da addu’ar Allah ya saka wa dukkanin wadanda suka bayar da lokacinsu da karfinsu wajen tabbatar da bukukuwan sallar sun gudana lafiya a jihar.

A tasa fannin, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala A. Muhammad  ya nemi jama’an jihar da su taimaka wa Gwamnati wajen samun nasarar gudanar da harkokin da suke gabanta.

Ya shaida cewar gwamnatinsa tana da tsare-tsaren masu kyau da ta zo da su, don haka ne yake mai nemai jama’an jihar da su mara masa baya domin ya kai ga cimma nasarorin da gwamnatinsa ta zo da su.

Wakilinmu ya shaida cewar a bisa al’ada ne kuma duk shekara, Mai Martaba Sarkin Bauchi da tawarsa sukan je gaisuwar sallah gidan Gwamnatin jihar, inda Sarkin ke zayyano wasu daga cikin matsalolin talakawarsa da neman gwamnatin ta sha kansu, a wannan shekarar ma na tsammanin hakan a ranar Laraba.

Exit mobile version