Karancin Abinci Illa Ne Ga Tsaron Kasa

Tun lokacin da aka fara rikicin manoma da makiyaya sai kuma al’amarin daya shafi tsaron gonakin manoma, da kuma aka maida hankali wuraren da suka saba da yin noma, sai kuma abin ya zama na damuwa, saboda hakan  na iya shafar abinci saboda ana iya samun karancin shi. Sannu a hankali kuma sai abin ya shafi harkar tsaron kasa, saboda irin halin da ake ciki wanda ke da bukatar a  kawo dauki, domin yanzu manoma suna tsoron zuwa gonakin su, musamman ma jihohin da suka dogara da aikin noma saboda shi ke samar masu da kudaden da suke biyan bukatunsu.

Tuni dai aka fara samun  karuwar farashin kayayyakin abinci, da kuma rashin aikin yi, ga kuma karuwar fatara, da kuma watakila Nijeriya idan ba Allah ne ya kiyaye ba,  Nijeriya na iya fuskantar shiga fari. Muna iya tunawa dai irin wannan matsalar ta kai wani mizanin wanda ba za a ci gaba da amincewa ba, ai gwamnatin ta dan yi bayani a kan shirin data ke yi na ta dauki ma’aikata3,000, a wani shirin da zata bullo da shi wanda zai taimaka wajen samar da tsaro a wasu wuraren da ake da matsalar tsaron, bugu da kari kuma gasu manoman ne. An dai sa ran daukar su matasan 3,000 kamar a dan diga ruwa cikin Teku ne amma kuma suna yi ma abin kallon wata dama ce, wadda za ayi amfani da ita, sai dai kuma  wasu nada shakku a kan yadda shi al’amarin yake, saboda  kuwa su manoman Nijeriya wasu sun shigo harkar ne saboda kawai su samu kudi.

Ga ire iren wadannan wadanda basu da wani abinda zasu yi, ko kuma suke yi da zasu samu kudaden biyan bukatar su, noma ne kawai saboda ya zama masu tamkar wani abokin rayuwa ne. Don haka shi wannan alkawarin na samar da ma’aikata 3,000 wadanda na noma ne, basu isa ba musamman ma, idan aka kalli shi al’amarin na tsaro. Saboda kawai ya zo  masu ne kamar  wani barawo wanda yake zuwa da dare wanda kuma ba wai yana daukar kayayyakin amfanin gonarsu kadai bane, amma har rayuwarsu da kuma sauran wasu kayayyakinsu, Wani abinda yake daure ma  kowa kai shi ne, a lokacin da ake shirin kara inganta abinda ya kasance ma mutum abokin rayuwa wato noma ko kuma sana’a,amma kuma sai ana kallon abin har sai watarana ya kai ga gagarar al’umma Allah ya dai kiyaye amin. Wuraren da al’umma suke noma  kamar dai yadda aka sani tun fil azal, abin ana samun koma bayan shi, wannan kuma ba karamin tasiri zai yi a kan al’amarin daya shafi bangaren tattalin arziki, da kuma yadda su rayuwar wadanda ke zama a irin wuraren zata iya kasancewa  ba nan gaba.

Shi wannan al’amarin da ake shirin yi ko shakka babu abin yana da amfami, saboda kuwa Hausawa sun ce  da rashin uwa ne akan yi uwar daki, wannan abu ne mai kyau da kuma bada kwarin gwiwa, saboda ko dai babu komi, ta banagaren daya ita gwamnati ta nuna da gaske take, tana kuma damuwa da halin da al’ummarta suke ciki. Ga wasu mutane wadanda suke ganin ya dace ayi maraba da kokarin da gwamnati take yi, saboda tayi maganin rashin tsaro wanda yake damuwar manoma. Halin da ake ciki yanzu shi ne wani babban al’amarin daya damu al’ummar Nijeriya shi ne, ba wai kawai harkar noma ta kasance cikin halin ni ‘yasu  ba, na tattalin arziki  ma , ya samu damuwa har ma shi wanda yake yin noman shi ma yanzu ana yi ma su kallon dan ta’adda. Dole a duba wannan da kuma samun yadda za a kawo maslaha, ita wannan kasa ta Nijneriya ba tana cikin yaki bane amma kuma wani abu wanda ke daure kai shi ne, sai kashe kashen mutane ake yi akai akai, ba domin komai ba sai saboda kawai su suna bukatar yin noma, don haka ake yi masu barazanar saboda a hana su zuwa gonakin su.

Wata hanya daya data rage saboda a samu kawo karshen rayukan da ake kashewa, wani babban abin so shi  ne, gwamnatoci ta bangarori daban daban, baya ga alkawari  na samar da ma’aikatan  gona wadanda zasu iya taimakawa wajen maganin yawan aukuwar rikici tsakanin manoma da kuma makiyaya.

Daya daga cikin matakan da muke ganin lokaci ya yi, mu bayar da shawara, shi ne a rika samun bayanai wadanda ko shakka babu zasu taimaka ma jami’an tsaro wajen gane bakin tsaren tun kafin ma matsalar ta taso. Sai dai kuma kash! Ba irin wannan abin ake yi ba yanzu, wanda kuma shi  ne yafi kamata ayi, saboda su jami’an tsaron wadanda ya kamata ace koda yaushe suna cikin shirin kota kwana, sai kuma ya kasance ana neman a mayar dasu tamkar abin yana neman yafi karfin su ne. Dalili kuwa wani lokaci al’amarin yana da daure kai da kuma ban haushi, maimakon su isa wurin da ake  ita gwagwarnayar tsakanin su ‘yan ta’adda da al’umma. Wani lokacin suna barin sai abin an kammala shi, daga baya kuma sai su iso wurin wanda a lokacin ba wani amfanin da hakan zata yi.

Wani abin bakin ciki kuma shi ne idan aka lura da kuma duk yadda aka kalli shi al’amarin, akwai rashin amincewa da juna, ba kuma wani abinda ke faruwa, amma kuma abinda ke faruwa sai kawai maganar zargin junan da ake yi. Ya yin da ake ta ci gaban da kallon duga dugan juna,su wadanda suke kallon kashe mutane kamar wani abinda suke so a rayuwars ne, sai su ci gaba da yin duk abinda suka ga dama.

Wani ma abu yanzu da ake yi saboda duk ma ko me nene zai faru ya dade bai faru ba, shi ne yanzu an fara sa al’amarin siyasa ciki, abin kuma wanda dole ne ya daure kai shi ne, an mayar da abin na kamfen ne, amma kuma gaskiya al’amarin ya rataya wuyan gwamnati ne, saboda ai ya shafi tsaro ne wadda kuma ai alhakin tane.

Harkar aikin gona wata abu ce wadda take da damar jawo hankalin masu sa hannun jari daga cikin gida da kuma  kasashen waje, amma kuma wani abin lura anan shi ne, ba tare  da an tabbatar da samar da tsaro ba, ba wani wanda ke sha’awar zuba hannun jarinsa, ko wanene shi, da zai amince ya zuba jarin shi, a wuraren da kamar ba a san darajar mutane ba, ana kashe su, su da dabbobinsu bayannan kuma a sace sauran kayayyakinsu. Wannan kuma yana zuwa ne duk a lokacin da gwamnati take kokarin, daukar babban mataki domin bunkasa bangaren na aikin gona. Ta hanyar sa milyoyin Naira musamman ma ta bangaren  masu noman shinkafa, inda babban Bankin kasa (CBN) yake taimakawa da bada rance.

Exit mobile version