Abdulrazak Yahuza Jere" />

Karancin Kiristoci Masu Ziyarar Ibada Na Barazana Ga Aikin Hukumarsu A Kaduna

2013 Christian Pilgrims: Nigerian Christian Pilgrims walking through Old City of Jerusalem , Israel yesterday. Photo by Gbemiga Olamikan.

Rashin samun isassun masu zuwa ziyarar Urshalima (Jerusalem) kamar yadda ya kamata daga shiyyar Kaduna ya zama babban kalubale ga makomar Hukumar Kula da Ziyarar Ibadar ta Kiristoci ta Jihar Kaduna.

Rahotanni na nunar da cewa karancin samun masu zuwa ziyarar ko wadanda za su dauki nauyinsu ya sanya ma’aikatan hukumar zaman kashe wando a bakin aiki.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Addinai ta jihar Kaduna, Injiniya Namadi Musa, wanda ya yi karin haske ga manema labarai a Kaduna kan lamarin, ya ce, rashin samun matafiya ziyarar urshalima (Jerusalem) ya sabba wa ma’aikatan hukumar zama haka babu abin yi.

A dalilin haka ne ma ya yi kira ga ’yan siyasa zababbu da ma masu rike da mukamai da su rika jajircewa su na daukar nauyin mabiyansu, domin su samu damar zuwa ziyarar ibadar. Ya ce, yin hakan zai tallafa wa hukumar domin ci gaba da gudanar da ayyukanta a Kaduna.

Injiniya Musa ya kara da cewa, idan a ka kwatanta Hukumar Kula da Jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna da ta Ziyarar Kiristocin ta fuskar gudanar da hada-hada abin ba a cewa komai, saboda duk shekara ma’aikatan Hukumar Alhazai ta jihar kullum cikin ayyuka suke har zuwa ranar da aka kammala jigilar Alhazai a fadin Tarayyar Nijeriya.

Rahotanni na nunar da cewa a shekarar bara karancin matafiya Urshalima (Jerusalem) ya sa ma’aikatan hukumar sun zama tamkar marasa aikin yi, ga shi kuma a wannan shekarar ma ta 2018 haka abin ya ke.

 

Exit mobile version