Karancin Kudi Ba Uzuri Ba Ne Na kin Biyan Ma’aikata Hakkokinsu – Ayuba Wabba

Daga Yusuf Shu’aibu,

Shugaban kungiyar kwadugo na Nijeriya, Ayuba Wanna ya bayyana cewa, rashin isassun kudade ba uzuri ba ne da wasu gwamnonin suke amfani da shi na rashin biyan karancin albashi ga ma’aikata.

Da yake magana lokacin da ake hira da shi a gidan talabijin na Channel Tb a ranar Litinin da safe, Wabba ya bayyana cewa, gwamnonin da ‘yan siyasa da ke rige da madafun iko su suke cinye kudaden gwamati su kyale ma’aikata suna hamma.

“Tun daga kan kanailoli har zuwa manyan masu mukamin a kasar nan ba a biyansu albashi kamar yadda gwamnatin ta tanada.

“Ya kamata gwamnatin ta bi tsarin yadda ake biyan ma’aikata. Farkon dauyin da ya rataya a wuyata gwnati wanda ya kamata gwamnoninmu su sani dai shi ne, tsaron rayukan mutane da kare jin dadin ma’aikata.

“Ta yaya za su ce jami’an tsaro masu kasada da rayuwarsu a koda yaushe su na yaki domin kasar nan ba za a kula da su ba?

“Ta yaya za su ce ba za a kula da ma’aikatamu ba da likitoci da masu jinya da dukkan sauran jami’an lafiya wadanda suke yakar cutar Korona ba za a ba su kulawar da ta dace ba.

“Wannan ba adalci ba ne kuma ba hanyar da ya kamata gwamnati ta bi ba ne.

“‘Yan siyasa nawa muke da su kuma nawa suke cinyewa? Wadannan ‘yan siyasa suke cinye kudaden kasar nan kuma ba sa gudanar da wani abu.

“Idan muka yi nazari a kan wadannan abubuawa da idon basira, abin da ake biyan ma’aikata bai taka kara ya karya ba, ‘yan siyasa ne ke lakume kaso mai tsoka na kudaden kasar nan.

A kwanakin baka ne ministan kwadugo da ayyukan, Chris Ngige ya yi barazanar daukan mataki a kan duk wani gwamnan da bai biyan sabon tsarin biyan albashi ba. Ngige ya bayyana cewa, za su tattauna da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Abubakar Malami a kan daukan matain shari’a kan gwamnonin da ba sa iya biyan sabon tsarin karancin albashi.

Exit mobile version