Bauchi, " />

Karancin Lantarki: Al’ummar Liman Katagum Sun Roki Gwamnatin Bauchi

*Kusan Shekaru Biyu Ba Mu Ga Hasken Lantarki Ba, A Cewarsu

Mazauna garin Liman Katagum da ke Bauchi sun koka bisa shafe kusan shekaru biyu ba tare da tozali da hasken wutar lantarki ba a sakamakon karyewar layukan wutarsu da suka yi tsawon lokaci.

Mazauna yankin sun ce wutar lantarki dai na daga cikin ababen more rayuwan al’umma, kan haka suka ce akwai gayar bukatar kamfanin samar da hasken lantarki ta JED tare da gwamnatin jihar da su dubi bukatar nasu tare da gyara musu hanyoyin wutarsu don su ma su ci gaba da amfanuwa.

Da ya ke tattaunawa da wakilinmu Munhaminna Aliyu Imam, daya daga cikin ‘yan Liman Katagum a jiya, ya shaida cewar dubban jama’a ke rayuwa a wannan garin, inda ya ce a sakamakon matsalar harkokin kasuwanci da dama sun ja da baya sakamakom rashin samun hasken lantarki.

“Mu na son mu roki Gwamnatin jihar Bauchi da ta dubi garin Liman Katagum da idon rahama (garin da tafi ko wacce gari girma a cikin karamar hukumar Bauchi) amma yau a ce mun shafe kusan shekaru biyu ba wuta abin damuwa ne matuka.

“Don haka mu na roko ga gwamnatin da ta gyara mana wutan lantarki wanda aka shafe kusan shekara biyu babu. Matsalar wutar ta samu asali ne sakamakon faduwan fol-fol na wayoyin wuta  da suke shigar da wutan cikin garin.

“A shekarar bara kafin saukan tsohon Gwamna yayi kokarin gyarawa an fara aiki sai aka samu iska da guguwa mai karfi da ya sake kayar da fol-fol na wayan lantarki, to har zuwa yanzu ba’a sake kula wajen ba, wanda mu kuma hakan na ci mana tuwo a kwarya, don haka muna amfani da wannan damar wajen rokon gwamna Bala Muhammad da ya dubu bukatarmu ya kawo mana dauki,” A cewar Imam.

Munhaminna Aliyu Imam daga bisani sai ya shaida wa gwamnatin cewar aikin nasu ba wai zai ci wasu maguden kudade bane, “Layukan wutar ne suka samu matsala. Amma sauran kayyakin wutarmu duk suna nan. Mu dai roko muke idan aka duba dumbin jama’a da suke rayuwa a wannan garin ya dace a dubemu da idon rahma,” Aliyu ya sake roka.

Daga karshe sai ya ce, “Ko ta fuskacin harkokin kasuwanci ya dace a duba mana domin matasa suna samun abinda suke rufa ma kansu asiri akwai masu nika,  da masu sayar da ruwan sanyi,  aski, da dai sauran masu amfani da wutar,”

Wata ma da take zaune a Liman Katagum mai suna Aisha Musa (Maman Fati) ta jaddada bukatarsu ga gwamnatin da cewa, “A irin wannan lokacin ma da ake fama da zafi muna rokon a tausaya mana a gyara mana wutar lantarkimu. Muna da kwarin guiwar Gwamma Bala Muhammad zai sauraremu kuma zai ji wannan korafin domin shi gwamnan talawa ne,” A cewarta.

Exit mobile version