Connect with us

RAHOTANNI

Karancin Ruwan Sha: Dan Majalisar Dala Ya Nemi Gwamnati Ta Dauki Matakin Gyara

Published

on

Dan Majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Dala a majalisar Dokin jihar Kano, Hon..Lawan Husain ya mika kudurin jan hankalin Gwamnatin jihar akan ta kawo dauki don magance matsalar tsananin karancin ruwa da ya addabi Karamar Hukumar Dala, da ma yawancin sassan Kananan Hukumomi da ke kwaryar Birnin Kano.

Ya ce, matsalar karancin ruwan ya kansa magidanta da yara da mata fitowa da sassafe su fito suna neman mai tallar ruwa a  jarka na sayarwa, wani lokacin ana saida jarkar ruwa daga N50 zuwa N100 wannan yakan janyo hana yara zuwa makaranta ko su je a makare.

Hon..Lawan Husaini Cediyar ’Yan Gurasa ya ce, wannan tararrabi na rashin ruwa na sa magidanta kwanciya da tunanin sama wa gidansu ruwa kamar yadda suke tunanin sama musu abinci haka su ke tunanin samun ruwan sha da ruwan da za su yi wanka da sauran hidindimun yau da kullum, wanda hakan ya ja hankalinsa ya yi wannan kira ga Gwamnatin.

Ya ci gaba da cewa a duk Kananan Hukumomi guda Takwas na cikin Birnin Kano babu ruwan sha, don haka a yi kokarin inganta harkokinsa, za a inganta hanyoyin da za a inganta ruwan sha.

Ya ce a lokacin da ya gabatar da kudurin a Majalisar, an yi muhawara sosai, kuma gida ya amince, don haka suna fata mai girma Gwamnan Kano zai dubi abin duk da cewa matsala ce ta tsawon lokaci da ta ke gadajjiya, suna fata daga Gwamna, in Allah ya yarda zai taimaka a samo bakin zaren a kawo karshen al’amarin.

Dan Majalisar na Dala ya ce Karamar Hukumar ta fi kowacce yawan jama’a da in ka za ga sai ka ga an yi cincirindo a bakin motar ruwa da ake kaiwa wasu Unguwannin.

Hon. Lawan Husaini ya ce wannan kira ne suka yi ga Gwamnati, wanda alhakinta ne sauke wannan nauyi na al’umma, kuma za su ci gaba da jan hankalin Gwamnati don daukar mataki a kai.

Advertisement

labarai