Connect with us

RAHOTANNI

Karancin Ruwan Sha: Mai Gudi Ya Musanta Dakatar Da Dagaci A Yobe

Published

on

Mai (Sarkin) Gudi a jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwo Ibn Madubu Khaja, ya karyata labarin dakatar da daya daga cikin dagatan sa; Lawanin kauyen Kadi, Abubakar Lumo biyo bayan wata fira da ya yi da wata kafar yada labarai, inda ya koka dangane da matsalar ruwan sha da yankin sa ke fuskanta.

Mai Gudi ya bayyana hakan, a wata sanarwar manema labarai, mai dauke da sa hannun sakataren masarautar, Musa Yakubu, inda a ciki ya karyata wani labarin da ke kai komo a kafafen sadarwa wanda ya nuna masarautar Gudi ta dakatar da daya daga cikin dagatan ta, ya ce wannan zance ne maras tushe da makama, wanda wasu maras kishi su ka kitsa shi tare da yada shi don cimma wata boyayyar manufa ta siyasa, don kawai a bata sunan masarautar.

Sanarwar ta kara da cewa masarautar Gudi ba ta taba daukar matakin dakatar da wani dagacin ta ba, kamar yadda jaridar Saharareporter ta yi zargi, wanda wannan zargi ne na rashin kan gado kuma wanda bai da ma’ana da ta yada a kafar sada zumunta, saboda haka sam masarautar Gudi ba ta da masaniya dangane da wannan kirkirarriyar karya.

“Bisa ga wannan na nake son inyi amfani da wannan kafa wajen tabbatar da cewa Mai Gudi bai dakatar da Lawanin kauyen Kadi ba.” Ya nanata.

Haka kuma ya bukaci jama’a su yi watsi da wannan zargi maras tushe da makama wanda bai faru ba. Sannan kuma ya bukaci masu yada labarai ta hanyar kafofin sadarwa na zamani da cewa ya dace su rinka amfani da matankadin tace labarai kafin su yada, kuma su guji bata suna.

“Har wala yau kuma, bisa ga hakikanin gaskiya, wannan kafar sadarwa ta shahara wajen yi wa jama’a daban-daban karairayi da sharri, wanda ba a kanmu su ka fara ba, saboda wannan labarin da su ka yada inda su ka nuna cewa wai masarautar Gudi ta dakatar da dagacin kauyen Kadi, yayin da wannan labarin bai faru ba Sam, zance ne na karya wanda aka kirkira don biyan wata manufa.” In ji Mai Gudi.

Ya ce, dakatarwa ba ta aikin masarautar Gudi ba ne, ya kara da cewa kuma a tarihi irin wannan dakatarwan bai taba faruwa ba a yankin sa ba.

Ya bukaci al’ummar masarautar Gudi su ci gaba da bayar da cikakken goyon bayan su ga gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni a kokarin sa na shimfida kyakkyan shugabanci.

Bugu da kari kuma, ya yi kira ga yan jaridun kasashen waje da na cikin gida wajen gudanar da gaskiya da yi wa kowa adalci a lokacin da su ke gudanar da aikin su na neman labarai, wanda hakan shi zai bayar da gudumawa wajen ci gaba da hadin kan kasa.

Advertisement

labarai