Connect with us

KIWON LAFIYA

Karancin Shayarwa Na Taimakawa Wurin Cutar Yunwa Ga Yara –Masana

Published

on

Wani kwararre a bangaren abinci Malam Sulaiman Mamman ya bayyana cewar yadda ba a samun kula da shayar da yara mama da kuma wasu abubuwan da zau taimaka, wajen cika gibin nonon, sune daga cikin matsalolin da suke addabar yara dangane da rashi isassun kayayyakin abincin da siuka kamata wajen taimaka ma yara.

Mamman har ila yau shi ne mai kula da bangaren abinci na Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Gombe, ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai na kasa, ranar Alhamis cewar mata biyar ne  a jihar wadanda suke yin amfanin da al’marin shyar da yara nono.

Kamar dai yadda ya kara jaddadawa shi ma wannan kiyasin an danganta shi ne da shekarar 2017, wato waniabinda ake amfani da shi a kasa da ake kira da suna Multiple Indicators Clustres Serby .

“Fara shayar da nono da wuri shine bayan da haihuwa da awa daya uwa ta far aba jaririnta nono.”

“Babban dalilin d ayasa ake yin haka shi ne a tabbatar da cewar shi jaririn ya samu colostrum, wato wata madarar nono ta farko wadda ta kunshi sinadaran da suke kawo kariya.”

Kamar dai yadda ya ce, kashi 21 na mata suke ke shayar da ‘ya’;yansu nono na wata shida, su kuma kashi 19 suna amfani da shayarwar gaba daya, su kuma kashi takwas suna shayarwa ne saboda shi nono ya maye wani abinci.

Ya nuna rashin jin dadin shi akan yadda har yanzun ba sa samu wani ci gab aba, donhaka ya yi kira da mata su fara ‘ya’yansu nono bayan awa daya da haihuwarsu.

‘Iyaye mata ya dace su ci gaba da shayar da ‘ya’yansu nono har zuwa wata shida, daganan kuma sais u fara basu abincin da zai maye gurbin nonon da ba a samu.

“Maganar ci gaba da shayar da yara shi ne lokacin da ake shayar dasu nono tare da abincin, da yake ba mai kauri bane.

Yin wannan zai taimaka sosai wajen matsalar da ake shiga ta rashin isasshen abincin daya kamata ga yara musamman ma a shekarar 2017 yara 170 ne suka mutu, a sanadiyar matsalar a jihar Gpmbe.

Babban jami’in al’amarin daya shafi abinci ya yi kira da gwamnatin jihar Gombe da su dauki wani matakin da zai maganin matsalar, wajen kafa cibiyoyin kula da matsalar a Gombe.

Kamar dai yadda ya kara bayyanawa a halin da ake ciki akwai wurare hudu da suka hada da Gombe da  Dukku sai Nafada da kuma Kaltungo wadda ke kulawa da kananan hukumomi 11 a jihar.

Mamman ya kara jaddada dole a kara yawan cibiyoyin saboda nisan da yake tsakanin su cibiyoyin da kuma wasu kananan hukumomin. Utane daga wasu wurare suna samunmatsala wajen kai ‘ya’yansu, zuwa dadaddun cibiyoyin da aka sani, wannan shi yasa ya dace a kara kafa wasu cibiyoyin saboda su kasance a dukkan kananan hukumomin 11.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: