CRI Hausa" />

Karfafa Dangantaka Tsakanin Sin Da Kasashen Afrika Na Iya Tunkarar Kowanne Irin Kalubale

Duk da cewa, cutar COVID-19 ta bulla kwatsam ba tare da gargadi ba, kamar kowacce annoba, sannin kowa ne kasar Sin ta samu gagagarumar nasara a yaki da ita, duk da yadda ta yi mummunan tasiri kan harkokin kiwon lafiya da zaman takewa da tattalin arziki da sauransu. Har kullum, kasar Sin tana kasancewa abun misali kuma abun dogaro, saboda managartan manufofi da tsare-tsarenta, da uwa uba shugabanci na gari da kaifin basira.

Ta kasance babbar kasa da ta san ya kamata. Domin ba ta boye duk nasarar da ta samu a kowanne fanni, tana mai yayata su domin sauran kasashe, musamman na Afrika, su koya don su ma su samu nasara. Haka kuma batun yake a nasarar da ta samu na yaki da COVID-19. Tun bayan da ta fara shawo kan annobar, a daya bangaren kuma, annobar ta fara yaduwa a duniya cikin sauri, kasar Sin ta fara yayata dabarun da gogewar da ta samu a yakin da ta yi da ita. Kuma tun daga wancan lokaci ta fara gabatar da bukatar hadin gwiwa domin shawo kan cutar.
Ko a jiya Litinin, yayin zantawar mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da takwaransa na Habasha, Gedu Andargachew, bangarorin biyu sun amince da karfafa dangantaka da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen yaki da annobar COVID -19. Wannan ba shi ne karon farko da Sin ta bayyana kudurinta ba, domin tuni ta fara aiwatar da su a aikace, la’akari da yadda ta tura kayayyaki da na’urorin da za su taimakawa kasashen nahiyar yaki da cutar. Kana ta tura kwararrun jami’an lafiya domin musayar ra’ayi da horar da takwarorinsu na Afrika dabarun tunkarar cutar da jinyar marasa lafiya. Haka zalika, ta gudanar da taruka da dama ta kafar intanet kan batun. Na baya-bayan nan shi ne taron da aka yi ta kafar bidiyo tsakanin shugabannin kasar Sin da takwarorinsu na Afrika, wanda Shugaban Xi Jinping ya jagoranta da kansa a ranar 17 ga wata. Kuma bayan kammala taron, dukkan bangarorin sun amince cewa, hadin gwiwa ce za ta kai su ga cin galaba.
Bisa la’akari da gargadin da Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO ya yi a jiya cewa, annobar ba ta yi ko kusa da tafiya ba, hadin gwiwa da musayar ra’ayi da dabaru da goyon bayan juna, su ne hanyoyin da suka dace da yaki da ita. Wannan kuma ita ce kiran da kasar Sin da ma Majalisar Dinkin Duniya suka dade suna yi.
Duba da yadda ta haifar da gaggarumar barazana da dan Adam bai gani ba cikin shekaru masu dimbin yawa, yadda za a ci nasara kan kwayar cutar, abu ne da ya tsaya a zuciyar kowace kasa da gwamnati. Kuma hanya mafi dacewa ita ce hadin gwiwa da goyon bayan juna. Kamar yadda masu iya magana kan ce, “hannu daya baya daukar jinka”, ci gaba da karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika na da makoma mai haske ba kadai ga shawo kan cutar ba, har ma da farfado da tattalin arzikin nahiyar Afrika da samar da ci gaba mai dorewa kamar yadda ake muradi. Kuma tasirin wannan hadin gwiwa, zai shafi duniya baki daya.
Hadin gwiwa da dangantakar Sin da Afrika, ka iya jurewa da tunkarar duk wata annoba ko kalubale, domin sun kasance masu dogaro da juna a lokacin farin ciki da akasinsa, wanda alamu ne dake nuna tubali mai karfi na mutunta juna da adalci da tabbatar da daidaito da aka gina su a kai. (Faeza Mustapha)

Exit mobile version