An gudanar da babban taro kan kiyaye tsaron harkokin sadarwa da masana’antu na kasar Sin na shekarar 2020 a jiya Juma’a, inda aka gabatar da rahoto game da ci gaban da aka samu a bangaren tsakanin shekarar 2019 zuwa shekarar 2020. Bisa hasashen da aka yi, a bana, karfin kasuwannin kare tsaron harkokin sadarwa da masana’antu na kasar Sin zai karu zuwa RMB yuan biliyan 12.2.
Don gane da yadda ake amfani da na’urori masu kwakwalwa da tsarin sadarwa cikin ayyukan makamashi da zirga-zirga da wutar lantarki da sauransu kuwa, a halin yanzu, ana hada na’urori masu kwakwalwa, da harkokin masana’antu da na sarrafa kayayyaki da yanar gizo a tare, lamarin da ya sa, aka fara mai da hankali kan tsaron harkokin sadarwa da masana’antu, haka kuma, ake habaka kasuwannin bangaren.
Bisa kididdigar da aka yi, a shekarar 2019, karfin kasuwannin kare tsaron harkokin sadarwa da masana’antu na kasar Sin ya kai yuan biliyan 9.974. Kana, a bana, adadin zai karu zuwa yuan biliyan 12.2. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)