Alhussain Suleiman" />

Karin Kudin Fetur: Shugaban NATA Ya Shawarci Gamnatin Tarayya

Shugaban NATA

Babu shakka ba wanda zaim ce ya ji dadin karin kudin Man Fetur da gwamnatin kasar nan ke yawan yi musamman na baya bayan nan , kamar talakawa, amma duk da haka acigaba da yi mata kyakkyawan zato na alhairi.

Bayanin haka ya fito ne daga shugaban kungiyar masu fasaha gyaran ababen hawa ta kasa NATA Injiniya Dakta Magaji Muhammad Sani, alokacin da yake tsokaci akan karin kudin Fetur da gwamantin ta yin a baya bayan nan.

Injiniya Dakta Magaji Muhamma Sani, ya jawo hankalin gwamnati cewa yana da kyau ta san halin da talakawan kasa suke ciki musamman na matsin rayuwa , dukm lokacin da aka yi karin kayan masarufi akasuwanni su kan yi tashin gwauron Zabi, tare kuma da karin kudin tafiye tafiye da sauran su.

Shugaban kungiyar ta NATA ya jaddadawa  manema labaran cewa amatsayin shin a shugaban kungiyar ta kasa ba ta ji dadin yawan karin farashin da gwamanati ke yawan yi ba , idan ya kasance dole sai ta yi ta rika la’akari ga marasa galihu .

Da yake tsokaci game da wata hukuma dake karkashin ma’aikatar kula da masa’antu ta kasa da ake kira NACDC da ta shahara wajen horar da koyon sana’oin dogaro da kai daban daban , sai shugaban ya nuna farin cikinshi akan kokarin da ta ke yi, wanda Alhaji Zailani Aliyu ke jagoranta.

Injiniya Magaji Muhammad Sani yay a nuna farin cikin shi game da yadda hukumar ta shiryawa mutane kimanin 150 horo akan yadda za su koyi gyran manyan motoci a Kano kwanakin baya, y ace dama hukumar ta NACDC kungiyar ta NATA suna tare da ita lokaci lokaci takan shirya masu irin wannan horo.

Sai ya yi kira ga hukumar da ta kara fadada shirin nata ya zuwa wasu bangarorin dake cikin kungiyar ta NATA, sannan ita kuma gwamnati ta kara baiwa hukumar hadin kai da goyon baya domin cigaba da gudanar da aikace aikacen da take yi wa al’umma.

Amatsayin shin a shugaban kungiyar ya nuna matukar damuwar shi game da yadda hanyoyin kasar nan suka yi matukar lalacewa , sai ya yi kira ga gwamanatin da ta taimaka ta gyara hanyoyin domin rashin gyaran na kawo yawaitar asaran rayuka da dukiyoyin matafiya sannan kuma masu aikata rashin gaskiya na amfani da lalacewar hanyoyin wajen aikata rashin gaskiya

Exit mobile version