Makonni biyu da su ka gabata, takaddama ta kaure tsakanin kamfanin man fetur na kasa NNPC da hukumar kula da farashin albarkatun man fetur ta kasa, dangane yunkurin karin farashin litar mai zuwa naira 212, wanda ya jawo martanin yan Nijeriya, al’amarin da ya tilasta wa hukumar PPPRA janye batun wanda shima kamfanin NNPC ya ce ba yanzu ba- kalmar da ke zama tamkar wanka da jirwaye.
Kwatsam kuma sai gashi an raka bako ya dawo, amma a kokarinta wajen kaucewa fuskantar fushin yan Nijeriya a shirin da take na aiwatar da kara farashin litar man fetur, a wani zaman da ta gudanar jiya Jummu’a, gwamnatin tarayya, ta hanyar shugaban kamfanin NNPC- Mele Kyari, inda ya fito fili a hukumance ta bayyana cewa ta gaji da biyan kumanin biliyan 120 na tallafin mai a kowane wata, wanda ta ce ya zama dole kara farashin man.
Har wala yau, Mele Kyari ya kara da cewa wadannan makudan kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa a tallafin man, sun zarta wadanda take kashewa; kimanin naira biliyan 70 a kasafin kudin 2021 a hukumar bayar da ilimin bai-daya (UBEC ), bugu da kari kuma sun zarta kudin da aka warewa aikin riga-kafi na kimanin naira biliyan 45.19.
Ya kara da bayyana cewa, saboda haka babu yadda za a yi Nijeriya ta ci gaba da sayar da litar man fetur a farashin naira 162 wanda ya zama dole litar man ta koma naira 234, domin ba zata ci gaba da biyan naira biliyan 120 a Kowane wata ba, na tallafin mai litar miliyan 60 da yan Nijeriya ke zukewa a kowane rana ba.
Kamfanin man fetur kasa- NNPC ya dage kan cewa ba za a yi karin farashin litar man fetur, sabanin wata sanarwar da Hukumar sanya ido kan farashin man a tarayyar Nijeriya ta PPPRA ta fitar wanda ta nuna cewa sabon farashin litar man zai koma naira 212.
Wannan ya na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin NNPC, gwamnatin tarayya su ka dora alhakin ga ‘tallafin man fetur’ tare da kafewa kan cewa farashin litar zai ci gaba da kasancewa naira162 har zuwa watan Afrilu, domin bai wa gwamnati damar zaman tattauna wa da kungiyoyin kwadago dangane da lamarin.
A hannu guda kuma, MD Kyari ya dage kan cewa babu makawa dole sai an kara farashin litar man, tare da shaidar da cewa kasuwa tafi alkali yanke hukunci, saboda haka a bar kyale kasuwa ta yi halinta dangane da kara farashin man a kasar nan.
Yanzu ana iya cewa kenan kamfanin NNPC ya sauya matsaya ta hanyar lashe aman da ya yi a baya, inda ya kafe kan cewa babu zancen kari, tare da shaidar da cewa farashin litar man ta na nan yadda yake a baya. Sannan kuma wannan martani ne ga sanarwar da hukumar PPPRA ta fitar na yuwar kara farashin litar man zuwa 212.6. Wanda bayan zazzafar muhawarar yan Nijeriya, wanda hakan ya tilasta goge sanarwar daga shafinta.
A halin yanzu, wacan dambarwar karin farashin litar man fetur fiye ma da yadda ake tsammani a baya na 212, wanda ko shakka babu hakan zai takura talakan Nijeriya tare da tabbatar da: mai kukan targade ne ya hadu da karaya, ta yadda karin farashin zai shafi kayan abinci da masarufi hadi da na sufuri a rayuwar yau da kullum. Har wala yau ta duba da halin matsin fatara da yan Nijeriya su ke ciki, wanda shi ne lokaci mafi dacewa talaka ya samu sassaucin rayuwa- karin zai kara zafafar halin matsin.
A gefe guda, karin farashin man zai kara jefa yan Nijeriya cikin mawuyacin hali da matsin rayuwa kana kuma wannan ya nuna tamkar gwamnati ba ta damu da halin da yan kasa suke ciki ba. Sannan kamar gwamnatin ba ta la’akari da abinda karin zai haifar ba a rayuwar masu karamin karfi, wanda baya ga karin kudin mota, kayan abinci da na masarufi, karin zai shafi harkokin noma a makamancin wannan lokaci wanda jama’a ke karkata ga harkokin noma don samun abincin yau da gobe.
Haka zalika, al’amarin karin ya fusata miliyoyin yan Nijeriya da tare da jawo tofin Allah tsine, saboda yadda karin zai kara munana halin matsin tattalin arzikin da talakan kasa ke fuskanta, wanda ya dace gwamnati ta dauki matakan saukaka yanayin, musamman yadda ake tabka zazzafar muwahara a shafukan sada zumunta na zamani.
Ga kadan daga cikin ra’ayoyin yan Nijeriya: “Ya lafiyar kura, balle kuma tayi hauka-nawa ne farashin kayan abinci kafin yanzu, me mu ke tsammanin a daidai wannan lokaci wanda maimakon a tsamar da yan kasa sai kara dulmuya su ake. Ko shakka babu karin zai shafi kayan abinci, masarufi da sufuri.”
“Har yanzu babu wani saukin rayuwar da matsakaicin dan Nijeriya ya samu, sannan wai ma shin, ta wace hanya gwamnati za ta taimaka wajen tsamar da talaka daga tsaunin talauci da fatara?”
“Wayyoo Allah, kawai yau mun wayi gari da karin farashin litar man fetur zuwa naira 212. Wannan ma fa wai kafin mu kai 2023. Ni tsorona ma mutum ya wayi gari nan gaba ace wasu sun taskace yan kadarorin da muka mallaka- da sunan kamuwa.”
Shima ga abinda wannan yake cewa, “Chab din, tashi na daga bacci da karin farashin litar mai zuwa 212 na yi tozali; labari mafi muni da nayi arba dashi. Gaskiya ina kira ga gwamnatin Buhari ta sauya wannan shawara, wallahi kafin hakan mu na cikin halin kaka nikayi fah.”
“Kun manta a 2015, a karkashin gwamnatin da ake zargi da cin hanci, fetur din naira 87 ce, amma sai gashi a 2021 karkashin gwamnatin canji, mai yaki da cin hanci, litar mai 212!”
Me Yasa Jam’iyyar APC Ta Ke Zawarcin Goodluck Jonathan Da Sanata Kwankwaso?
Daga Sunusi Mai Lafiya Babban zaben shekarar 2023 gab yake...