Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Karin Kudin Makaranta: Boren Dalibai Ya Sa An Rufe Jami’ar Ondo

An rufe jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Ondo dake Okitipupa bayan dalibai makarantar sunyi zanga zanga bisa karin kudin makaranta. A ranar 30 ga watan Afrilu an bukaci daliban su fice daga makarantar sannan su dawo ranar 20 ga watan Mayu.
Ragistaran makarantar, Mr. Felix Akinusi, a ranar Litinin a Okitipupa ya sanar da cewa mahukuntan makarantar sun yanke shawarar rufe makarantar har sai baba ta gani. Akinusi ya ce an yanke wannan hukunci ne don guje wa kar daliban su karya doka.
Daliban sun gudanar da zanga zanga bayan hukumar makarantar ta bukaci daliban su ci gaba da biyan N150,000 ga yan asalin jihar da N200,000 ga wanda ba yan jihar ba a matsayin kudin makaranta duk shekara.
A da kudin makarantar yana kasa da N100,000 kafin hukumar makarantar su kara kudin a zangon karatun da ya gabata. Sannan sun kulla yarjejeniya da daliban akan za’a rage kudin makarantar a zangon karatu mai zuwa. Ragistaran ya ce hukumar makarantar suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan karin kudin makarantar don kawo karshe wannan matsalar.
Har ila yau, ya kara da cewa wasu daga cikin daliban musamman yan aji biyu sun yarda zasu ci gaba da biyan sabon kudin makarantar amma daga baya shuka canja shawara. Sai suka zabi suyi zanga zanga maimakon su zo mu tattauna.
Akinusi ya ce ‘Mahukuntan makarantar sun yanke shawarar a rufe makarantar sakamakon ikirarin da daliban suka yi na ci gaba da zanga zanga. Mahukuntan sun yanke wannan shawarar ne don kare tare da guje wa daliban karya dokokin jami’ar har sai mun kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki.’
‘Zamu sanar da daliban ranar da zasu dawo makarantar bayan mun shawo kan wannan matsalar, ‘ inji Akinusi.
Bugu da kari, an kulle jami’ar Adekunle Ajasin dake Akungba Akoko (AAUA) sakamakon tashi doron zabin da kudin makarantar ya yi.

Exit mobile version