Hukumar KAROTA ta kama wani Inyamuri mai suna Mista Ekennah Okechuku da ya yi safarar kwalaye sama da guda 60 da ke dauke da tabar wiwi zuwa Jihar Kano.
An cafke wanda ake zargin ne a ranar Laraba, bayan da ya boye tabar a cikin motar safa. Kazalika, wanda ake zargin ya fito ne daga Jihar Imo tare da bayyana cewa yana safarar magunguna daga Jihar Legas zuwa Kano, inda yake kai wa kwastomominsa.
Haka zalika, Mista Okechuku sunansa na cikin jerin sunayen da Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) nema, bisa aikata laifin dillancin tabar wiwi zuwa Kano.
A yayin mika wanda ake zargin ga Kwamandan NDLEA, Shugaban Hukumar Karota Baffa Babba Dan’agundi ya ce Hukumarsa ta ba da umarnin sauya gurin zama na tashar motar Sabon Gari da ake kira (Ludurious Buses), saboda irin wadannan laifuka da ake aikatawa da irin wadannan motoci.
Ya ce, a baya Rundunar ta cafke wasu kayayyaki guda biyu na mutumin wanda ya yi amfani da dabaru wajen boye su a cikin kaya.