Daga Abubakar Abba
Cibiyar Afirka da Amurka wato (AAI) ta karrama Shugaban Bankin Zenith Mista Jim Obia, lambar yabo ta Shugaban kasuwanci ta shekarar 2017. Wannan karramar ba ita ce ta farko ba, da aka taba yi wa kwararren a kan harkar hada-hadar Banki har da samun lambobin yabo na kasa da kasa, an sha karrama shi wajen harkar kasuwanci na Banki.
Mista Obia an karrama shi ne a kan irin gudunmowar da ya jima yana bayarwa wajen harkar kasuwancin Banki da kuma tallafa wa al’umma. An mika masa lambar ta karramawar ce a taron da aka yi a Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Kasar Amuka.
Mista Obia wanda shi ne Babban Manajin Darakata na farko na Babban Bankin a kasar nan wajen harkar hada-hadar Banki an karrama shi ne, tare da shugaban Kasar Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban gudanar da harkar mulki na Kafar yada labarai da kirkira Nicole Amarteifio da kuma Bozoma Saint-John, Babban jami’i na Kamfanin Kirkira da fasaha.
Dalilin da ya sa aka raba lambobin yabon a taron na Majalisar Dnkin Duniya shi ne, don a nuna wa Duniya namijin kokarin da ‘yan kasashen Afirka ke yi, wajen habaka tattalin arzikin kasashen nasu.
Ana sanar da bada lambar yabon ce, duk shekara, don baje kolin mutanen da suke da hazaka a kasashen Afirka, kuma Cibiyar ta karrama mutane da dama da suka yi kokari wajen cika manufar ta, na inganta rayuwar al’ummar Afirka da na kasar Amurka.
An mika lambobin yabon ne, a taron cin abincin dare da manyan shugabanin dunya suka halarta da jakadojin kasashen duniya da manyan jami’ai.
Tun lokacin da aka kafa Bankin na Zenith kusan shekara 20, Obia yake jan ragamar shugabancin Bankin kafin ya aje aiki a watan Yulin shekarar 2010, inda kuma aka sake nada shi shugaban Banki a shekarar 2014. Shi mamba ne na tawagar tattalin arzikin kasa kuma har ila yau, mamba ne na Cibiyar masu zuba jari ta kasa da kasa.
Obia yana yin aikin jinkai na taimaka wa al’umma kuma shi ne ya kirkiro da Kwalejinsa mai suna ‘James Hope College’, Agbor, da ke da hedikwata a Jihar Delta.
Ya kuma kafa Gidauniyarsa mai suna, Jim Obia wadda manufar ta shi ne, taimaka wa wajen bayar da gurbin karo karatu ga marasa galihu, inda ta yaye dalibai da dama a kan fannin aikin likita da aikin injiniya da sauran su.
Obia kuma ya kirkiro da zubin hanyoyin kasuwanci da kungiyoyinsa ke kai, da suka hada da kafa sana’o’in hannu ga matasa don su zamo masu dogaro da kansu ta hanyar ilimin kimiyya.