Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Sakamakon lura da irin tallafi da gudummuwa ta son ci gaban zaman lafiya da kishin bunkasa al’ada da harahen Hausa, wasu kungiyoyi guda biyu na dalobao da na Hausawan Afirka suka karrama fitaccen dan kasuwar nan mai harkar canjin kudaden kasashen, Alhaji Bashir Usman Sani Gwale.
Wannan karramawa da aka yi masa ta Jakadan Zaman lafiya da kuma Barden Hausawan Afirka, Alhaji Bashir ya bayyana cewa wannan karramawa za ta zama masa tamkar wani karin kaimi ne wajen ci gaba da aikin nasa.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan karramawarda aka yi masa a wani gagarumin taro da aka gudanar a dakin taro na kwalejin ilimi na Sa’adatu Abubakar Rimi, wanda ya hada ‘yan uwa da abokan arziki da iyaye da shugabannin kungoyoyin, Jakadan Zaman Lafiyan, Barden Hausawan Afirka ya bayyana cewa matsayin da aka karrama shi da su za su kara masa ci gaba a kokarin da yake na hidinta wa al’umma da habaka al’adu da harshen Hausa.
Ya ce bai zaci wannan karramawa ba, don yana zaune ne sai ya sami kiran waya daga Kwalejin Sa’adatu Rimi nan ya sami bayanin daga Dokta Nafi’u na wata kungiya ta dalibai ta Arewacin kasar nan da suka zabe shi don karrama shi, Sannan kuma akwai kungiyar Hausawan Afirka da suma za su karramashi akan bunkasa cigaban harshen Hausa.
Ambasada Bashir ya ce wannan shine makasudin karramawar da akayi masa ta zama Jakadan zaman lafiya da kuma Barden hausawan Afirka wannan yazo masane sakamakon irin mu’amala da dangantakarsa take tsakaninsa da mutane, kamar yadda masu karramawar suka bayyana a cikin dalilansu na karramawar saboda sun bincika sun ga yadda yake kokari na tallafawa mutane musamman marayu da gajiyayyu a cikin al’umma dai dai gwargwadon halinsa.
Alhaji Bashir Usman Sani ya ce ba yanayin hidima ta taimakon al’umma ba ne domin a gani ko dan mutane su yaba masa ko kuma wata kungiya tazo ta bashi kyauta ko ta karrama akai bane, yana yine sabpda Allah kamar yanda addinin musulunci ya horesu dayi,kuma al’adarsu ta Bahaushe ta.son bakice tana kuma girmama bako kowane gari a Duniya yana cigaba da bakone in babu bako wannan gari bazai cigaba ba.
Ya ce kowane gari da a yanzu yake da cigaba za a samu akwai baki a cikinsa, don haka suna alfahari da al’umma musamman baki, kuma gwargwadon abinda Allah ya hore masa yana kakarin taimakawa kuma wannan shine abinda yasa wadanan kungiyoyi ma suka nemo shi sukayi masa karramawa.
Ambasadan Zaman lafiya Alhaji Bashir Usman ya yi nuni da cewa wannan jakadanci da aka ba shi na wakiltar zaman lafiya babban abu ne a halin da ake ciki yanzu kuma dama tun kafin wannan kakadanci kullum ta Allah a cikin kokarin yin sulhu da sasanta tsakanin al’umma yake don samun fahintar juna da daidaito dan dinke baraka data taso.
Ya ce har tattaki yakan yi zuwa wasu garuruwa dan samarda sulhu da kyautata mu’amala tsakanin mutane da sukeda sabani,wannan kuwa suna yine yine kamar yanda suka taso sukaga iyayensu na yi Suna cudanya kansu da kowa da mai arziki da marasa karfi duk nasu ne, kuma ko’ina suna tashi suje domin samarda daidaituwa da sulhu da zaman lafiya, saboda haka wannan abu da yazo na ba shi jakadan zaman lafiya da yardar Allah zaiyi kokari iya bakin kokarinsa dan ganin ya taimaka yana rokon Allah ya taimakeshi wajen cimma nasara.
Barden Hausawan na Afirka.Alhaji Bashir Usman yayi nuni da cewa dama tun kafin wannan matsayi kullum suna kokarin bunkasa harshen hausa domin duk inda ya shiga a kasashen Duniya yana al’fahari da Harshen hausa duk inda yake yana cewa shi Bahaushene,kuma duk inda yaga Bahaushe baya wata magana dashi sai dai harshen Hausa.
Ya ce daga cikin abokansa da suke kasashen Turai idan yaje yana yawan jan hankalinsu akan kada su yarda al’adarsu da harshensu na hausa ya subuce suyi kokari lallai ya’yansu su danfaru da wannan harshen na hausa da al’adarsu , domin shine abinda za suyi alfahari dashi, karsu bari al’adarsu ta barsu,domin duk wanda ya bar al’adarsa sai yayi dana sani,wacce zai je ya aro a can inda yake baza suyi alfahari dashi ba.Sannan inya bar tasa an manta dashi kenan sannan bai barwa kansa da ya’yansa gado mai kyauba.
Ya ce dama hausa tasuce da yardar Allah zasu cigaba da kulada bunkasata duk inda suka sami kansu, suka kuma sami Bahaushe a wajen duk inda yaje a kasashen Duniya.
Yace za su yi kokari su tafi tare su tsira tare,ta yanda al’ada da harshen hausa zai kara bunkasa.
Jakadan zaman lafiyan Barden Hausawan Afirkan, Alhaji Bashir Usman Sani ya ce wannan karramawa da aka yi masa zai kara masa wani karin kaimi ne da karsashi da himma a gare shi ta yadda da yardar Allah za su ci gaba da dorawa kan irin abinda suke fiyeda na baya dan kara bunkasa cigaban hausa ta yanda zai amfani al’ummar hausawa a ta yanda za’ayi alfahari da su.
Alhaji Bashir Usman Sani ya nuna mutukar jin dadi da farin ciki da godiyarsa ga Allah bisa wannan ni’ima da yayi masa, domin shi kadaine yake yabon bawansa kafin wani ya yabeshi, sannan. ya godewa kungiyar Hausawan Afirka da da ta dalibai bisa hobbasa ta zabo shi da suka yi suka karrama shi.