El-Zaharadeen Umar" />

Karramawar Gidauniyar ZIK Ga Gwamna Masari, An Dora Abu A Muhallinsa

08062212010

Sannu a hankali mutuncin da martabar jihar Katsina sun fara dawowa a Idon duniya, ta fuska da dama sakamakon jajircewa da kuma dagewar gwamna Aminu Bello Masari na ganin haka ta tabbata cikin nasara.

Jihar Katsina ta sha fama a hannun marasa kisa, ta yi doguwar suma, wanda take in banda mutane irin su Gwamna Masari ba, to sai dai ayi hakuri da dawowar mutuncinta da ya zube sakamakon yadda komi ya lallace ta zama koma baya babu wani abu guda daya da yake tafiya dai dai.

Aiki bakon raggo,! Kowa ya ga ji, bai saba ba,! kyakkyawar niya da manufofi da gwamna Masari ya zo da su, sun taimaka matuka gaya wajan ganin jihar Katsina ta fara murmurewa daga bakin ciwo da ya addabeta daga hannu ‘yan bani na iya, da man tun kafin zuwansa yana da tsare-tsare na dawowa da martabar jihar Katsina, (Restoration Agenda)

A fili yake cewa tun kafin Gwamna Aminu Bello Masari ya samu nasasar cinye zabe ya kafa wasu kwamitoci wadanda za su duba su yi binciken kwa-kwaf da zai taimaka masa ya samu haske ta inda zai fara kaninkacin wannan jaha da ta fada hannu masu kuruciyar bera a zamanin baya.

Rantsar da shi ke da wuya, bayan da ya tabbatar yanzu yana da majalisar zartarwa wanda ita ma take a shirye domin taimakawa a kawo gyara a jihar Katsina, sakamakon binciken da kwamitocin nan suka yi, aka dauka aka fara aiki da shi  wanda yanzu ake ganin alfanin abun.

Wannan yana matsayin shinfida gane da hanyoyin da wata cibiyar bincike da ke jihar Legas ta gudanar da nata bin diddigin domin gano wanene Aminu Bello Masari kuma wace irin gudunmawa ya bada a matsayinsa na gwamnan jihar Katsina a shekarar 2017 da har ta zabe shi a matsayin gwarzanta na shekarar 2017 ta karrama shi a jihar Legas.

Abinda na ke son in fada anan shi ne, duk wanda zai karrama gwamna Masari ko kuma jihar Katsina anan gaba, ga hanya mafi sauki da zai bi ita ce hanyar da waccan cibiyar bincike mai suna ‘’Public Policy Reseach And Analysis Center’’ ta bi domin kaucewa san rai da cuwa-cuwa.

Babu shakka wannan kyauta da aka yi wa gwamna Masari ba shi kadai aka yi wa ita ba, jihar Katsina ce ta samu nasara domin idan da ace mutanen Katsina ba su shi ba shi damar zama gwamna ba, sai dai a bashi wannan kyautar a matsayinsa na Aminu Bello Masari ba gwamnan jihar Katsina ba.

Da man dai wannan cibiya ta saba gudanar da lakca duk shekara domin bayyana wasu daga cikin halayyar Marigayi Dakta Nmandi Azikiwe da kuma tunawa da wasu abubuwan da ya bari na alheri. Daga baya kuma cibiyar suka yi tunanin bullo da bada kyauta ta musamman ga wasu kebabun mutane da suka taka mahimmiyar rawa wajan cigaban al’ummarsu.

ita dai wannan karramawa da aka yi wa gwamna Aminu Bello Masari tare da wasu manyan mutane da suka bada gudunmawa ta fannoni daban-daban ta biyo bayan wani bincike na musamman na wata cibiyar bincike da tsare-tsare da kuma yin fashin baki ta gudanar inda daga karshe ta bayyana gwamna Masari a matsayin gwamnan da ya kawo canji a fannoni da dama da suka hada da kawo cigaba a rayuwar jama’a da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen jihar Katsina.

Cibiyar ta kara da cewa Masari ya dage kai da fata wajan ganin martabar jihar Katsian ta dawo a idon duniya, ta ce wannan kokari na shi ya zuwa yanzu ya fara haifar da da mai ido, kuma jama’a tuna suka fara yin alkalanci akan wannan cigaba da ya kawo.

A wannan cibiya Ferfesa Jibrin Aminu shi ne baban mai bada shawara sai kuma shugabanta wanda yake sananne ne, wato Cif George Obiozora wadanda dukkaninsu masana ne game da yadda ake zaban mutun wanda ya bada gudunmawa kafin a ba shi wata kyauta ko girmamawa, wannan yana daga cikin abubuwan da gwamna Masari ake yawan yin masa tambihi akan sa.

A jawabansu shuwagaban wannan cibiya Ferfesa Jibril Aminu da Ferfesa George Obiozor sun bayyana cewa Masari mutun ne da yake da ilimin siyasa tsawon lokaci wanda hakan ne ke yi masa jagora akan nasarar da yake samu wajan yin ayyukan cigaba ga al’ummarsa

Haka kuma sun kara da cewa Masari ya yi kokari wajan kawo sauyi na yadda ake tafiyar da gwamnatin jihar Katsina a baya, acewarsu hanyoyin da ya dauka na tunkarar matsalolin jiha tare da kawo cigaba da abubuwan more rayuwa ya budewa katsina wani sabon sashi a idon duniya kuma a siyasance.

Ferfesa Jibril Aminu ya ce tsayawar da Masari ya yi kai da fata wajan aiwatar da manufofinsa na dawo da martabar jihar Katsina idon duniya abu ne da yakama a duba, kuma wannan kyauta ko karramawa an dora abu a muhallinsa.

Wasu daga cikin wadanda aka karrama wajan  wannan gaggarumin biki sun hada da gwamna Aminu Belo Masari na jihar Katsina wanda shi ne uban gayyar da gwamna jihar Ribas, Barr. Nyeson Wike da Cif Audu Ogbeh Ministan Ayyukan Gona na tarayyar Najeriya da kuma Mista Ernest Ebi shugaban Banki Fidility.

Sauran sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar CAN, Cif Adebisi Akende da Babban Darakta a ma’aikatar NNPC Dakta Mai Kanti Baru da Dakta Adedeji Adeleki shugaban kamfanin Pacific Holding Limited da uwargidan gwamnan jihar Anambra, Cif Ebelechukwu Obiano da Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar

Daga cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen biki akwai gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu da gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar, da gwamnan jihar Sakwato, Aminu Waziri Tambuwal, haka kuma an samu wakilcin masu martaba sarakunan Katsina da kuma Daura wadanda ‘ya ‘yan su suka wakilta a wajan wannan taro.

Kasaitaccen bikin wanda aka shirya shi a cibiyar Cibic Center da ke rukunin unguwanin bictoria Inland da ke jihar Legos ya samu halartar dubbin masoya da magoya bayan gwamna Aminu Bello Masari daga jihar Katsina da suka hada da ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma masu rike da mukamai a gwamnatance.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro na tarihi sun hada da mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu da Sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammed Inuwa da ‘yan majalisar Dattawa da ‘yan Majalisar wakilai da kuma ‘yan majalisar dokoki ta jihar Katsina da masu baiwa gwamna shawara a matakai daban-daban

Akwai mutane irin  su babban alkalin alkalai  mai Shari’a Musa Abubakar Danladi da shugaban kamfanin Mad Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Shitu S. Shitu da sauran manyan masu fada aji tare da shuganan Jam’iyyar APC na kasa mista Jonh Oyegun.

Shima mai gayya mai aiki, da yake magana a madadin wadanda aka karrama gwamna Aminu Bello Masari ya nuna jin dadi da godiya da wannan cibiya da kuma wadanda suka shirya wannan taro domin karrama su.

Masari ya bada tabbacin cewa wadanda suka shirya wannan biki ba su yi san ran su ba, ya ce ya yi farin ciki da wannan girmamawar da ta zama babu san kai acikin, amma da gani an sa tunani da hange nesa kafin a zabe su a karrama su.

Ya kara da cewa wadanda aka zaba aka karrama za su yi amfani da wannan damar su yi abinda ya kamata wajan cigaba da yi wa jama’ar su aiki wanda anan gaba zai zama wani abin koyi ga wasu da za su iya samun wannan karramawa mai girma. Daga karshen ya yi wa kowa fatan alheri

Gudunmawar da wasu masu kishin jihar Katsina suka bada domin ganin wannan taron ya yi nasara abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, domin kuwa Katsinawa mazauna jihar Legas sun yi kokari so sai wajan ganin gwamna Masari da mutanen jihar sun samu nasarar wannan taro.

Suma ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da suke zaune a Katsina ba a bar su a baya ba, domin kuwa sun tsaya ba zaune ba tsaye, Musamman sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa da ya sa ido domin ganin ba a samu wata matsala ba.

 

Exit mobile version