Shugaban riko na jami’iyyar APC gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ayyana ranar 26 ga watan Fabrairun gobe a matsayin ranar da jam’iyyar za ta gudanar da babban taron ta na kasa. Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a wajen taron mata na jam’iyyar wanda aka gudanar a yau Talata a Abuja.
Wannan sanarwar ta Mai Mala ta kawo karshen cece-kuce da aka jima ana yi kan batun babban taron jam’iyyar. Inda aka tsawaita wa Mai Mala din wa’adin shugabancin riko na jam’iyyar.
Mai Mala ya shawarci mata ‘yan jam’iyyar da su fito kwansu da kwarkwata don kada kuri’a da ma tsayawa takarar mukaman jami’yyar wanda a cewarshi take da membobi kusan miliyan 40 a fadin Nijeriya.