Connect with us

Madubin Rayuwa

Karuwanci A Manyan Makarantu Da Hatsarin Kamuwa Da Cutar Ƙanjamau (HIV/AIDS)

Published

on

Cigaba da yawaitar karuwanci a cikin manyan makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, babbar matsala ce da ta ke buƙatar ‘Yan Nijeriya gabaɗaya su farka daga barci su maida hankali a kai su yi duk abin da ya dace domin magance wannan matsala. Masu iya magana sun ce “matasa su ne shugabannin gobe”, su ne za su jagoranci al’umma su kuma tsara wa jama’a manufofi da tsare-tsare a rayuwa tagaba. Saboda haka idan ya kasance matasa suna faɗawa cikin harkar karuwanci da miyagun ɗabi’u, to shakka babu ƙasa ta na cikin hatsari mai girma.

Saboda maƙudan kuɗaɗen da ake samu a wannan haramtacciyar sana’a, waɗannan rukuni na karuwai a manyan makarantun gaba da sakandire kan samu kaya na alfarma da abubuwan bajinta daga abokan hulɗarsu domin nuna bajinta da kece raini a tsakanin abokan karatunsu. Idan ka ziyarci wuraren kwanan ɗalibai mata (Hostels) a manyan makarantun gaba da sakandare da daddare, abu na farko da zai fara baka mamaki shi ne manyan motoci na alfarma da za ka gani waɗanda suka zo domin su ɗauki ‘ƴan mata ɗalibai su tafi wuraren casu ko fati da sauran yawon shaƙatawa da su. Hatta ɗalibai mata a yanzu sun kasance dillalan mata ga masu dukiya su na biyansu su samar musu da wadatattun ‘ƴan mata ɗalibai.

 

Ta’azzarar matsalar karuwanci a tsakanin ‘ƴan mata ɗalibai, abin damuwa ne matuƙa sannan kuma gagarumar matsala ce wacce ta ke neman ta zarce sauran matsalolin da ake fama da su a cikin al’umma, kamar matsalar ƙungiyoyin asiri da matsalar fashi da makami da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ke addabar manyan makarantun ƙasa.

Wannan burin samun dukiya ta haramtacciyar hanya da kuma fidda tsammani daga mafi yawan ‘Yan Nijeriya musamman ma waɗannan ‘ƴan mata da ke karatu a manyan makarantun gaba da sakandire, abubuwa ne da su ke sanya su faɗawa aikata fasadi da zinace-zinace ba tare da tunanin kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki “ƙanjamau”, (HIB/AIDS) da sauran miyagun cututtuka masu kisa da ake kwasa ta hanyar jima’i ba.

Rashin tarbiyya a makarantu matsala ce da ke jagorantar taɓarɓarewar al’amura a manyan makarantun gaba da sakandire, a mafi yawan lokuta Jami’o’i kan ba da kariya ga masu dukiya da suke aikata fasadi da ‘ƴan mata ɗalibai ta hanyar girmama su da lambobin yabo na digirin girmama da kuma ɗaure musu gindin cigaba da lalata da ‘ƴan mata. Muna cikin hatsari mai girma a wannan ƙasa matuƙar ba mu tunkari wannan matsala da gaske mun murƙushe ta ba. Amma tambayar ita ce; wa ke samar da dandalin cigaba da gudanar da wannan, a lokaci guda zai iya ya kasance ‘ƴan siyasa, masu riƙe da madafun iko da attajirai na daga cikin manyan masu taimaka wa cigaba da bunƙasar wannan mummunar sana’a a muhalli na farko.

 

Waɗanna su ne ya kamata a ce sun kasance ginshiƙan masu tarbiyyar gina al’umma, sai dai a yanzu sun zamto masu rusawa. Saboda haka ya zama wajibi ga iyaye su sanya ido sosai a kan ‘ƴa’ƴansu tare da ba su kykkyawar tarbiyyar da za ta haska musu hanyar da za ta jagorance su ko da ba sa a tare da su.

Masana halayyar ɗan adam sun tabbatar da cewa cigaba da ɗorewar matsalar karuwanci a manyan makarantun gaba da sakandire, matsala ce da za ta taɓa nagarta da darajar matasa masu tasowa waɗanda za su kasance shugabannin ƙasa a rayuwa tagaba. Haka zalika matasa ‘ƴan mata masu tasowa su na ɗaukan kaso mai yawa na adadin jama’ar ƙasa. Cigaba kaɗan za mu tsammata daga gare su idan ya kasance su na faɗawa cikin zinace-zinace da fasadi.

Sannan daga Allah ne; babu wani abu da ke sanya kokwanto ga iyaye kan halayyar ‘ƴa’ƴansu musamman ma idan aka zo batun kamewa daga aikata zina. Idan ya kasance yarinya an hore ta kan jin tsoron Allah da girmama sauran mutane da kuma kallo jikinta a matsayin ayar Allah ba za ta samu ruɗu da matsin lamba ba.

Duk yadda za a yi, ya zama wajibi a gudanar da bincike a cikin birane a gano manyan makarantun da ake aikata wannan harka ta karuwanci. Domin karuwanci a manyan makarantun gaba da sakandare a yanzu ya wuce yadda ya ke ada, a yanzu karuwanci ya zama kasuwanci na zamani da ake gudanar da shi cikin tsari, kuma ba wai iya yara mata ɗalibai ne kawai su ke yi ba har ma da yara maza ana saduwa da su kamar mata domin samun abin duniya.

Babu wata ƙasa da za ta tsira ko ta samu wani gagarumin cigaba idan ya kasance matasanta masu tasowa waɗanda ake da yaƙinin su ne shugabannin gobe ba su da kyawawan halaye da ɗabi’a masu kyau. Babu wani abu da za su iya amfanawa ƙasa da al’umma saboda munanan ɗabi’unsu sun rusa martaba da kima da darajar al’umma ta hanyar karya ginshikin da ya haɗa su da jama’a. Har wa yau mu na cike da fata da addu’ar yin bankwana da waɗannan matsaloli a manyan makarantunmu tare da fatan ganin an gina tushen al’umma mai nagarta da kyawawan halaye da ɗabi’u.
Advertisement

labarai