Connect with us

KIMIYYA

Karuwar Dogaro Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Barazana Ce Ga Lafiyar Mutane

Published

on

Kirkiren kimiyya da fasaha ya saukaka mana harkokin gudanar da rayuwa ta hanyoyi daban daban, zaka iya isar da sako ga dubbai ko miliyouin jama’a nan take ta hanyar latsa wani wuri a jikin wayarka ko kwamfutarka.
Sai dai abin takaicin shi ne mutane da dama na dogara gaba daya a rayuwarsu ga hanyoyin sadarwa na zamani abun dam asana kimiyya ke kira “Digital zombies” Kalmar da ake amfani wajen kiran mutanen da suka dogara kacokan ga kafafen sadarwa na zaman wajen gudanar da rayuwarsu.
Rahotannin da dama sun nuna cewa, matsanancin amfanin da na’urorin kimiyya da fasaha na iya haifar da matsaloli ga lafiyar dan adam, matsaloli kamar yawar damuwa da rashin kwanciyar hankali da ciwon ido da sauran lalurori. Wadannn rahoton sun bayar da karfi ne a kan maganan cewar, duk abin da ya yi yawa zai iya zama matsala.
Matsanancin kamuwa da amfani da kafafen sadarwana zamani ba kai ta’alaka bane ga masu amfani dasu na kasashen da suka ci gaba har ma da sauran kasashe masu tasowa. Wani abin dya kamata kowa ya gane shi ne mutum yana iya kamuwa da kafafen kimiyya fasaha ba tare da mutum ya gane cewa ya shiga matsalar ba, musamman ganin yawan na’urorin da mutane ke tarawa a gabansu a wannan zamanin.
A wannan zamanin yana da sauki ka ga mutane suna yin wasu abubuwa masu mahimaci kamar tukin mota amma suna kokarin yin kaya duk da dimbin hatsarin da yin haka ke iya kawowa ga rayuwa.
A kwai rahotannin mutanen da suka rasa rayukansu a hastsarin mota ko suka fada ramuka saboda sun nutsa cikin mu’amala da naurorin dake hannusu.
A kwai kuma labaran yadda jigin kasa ke nike matasa a sassan duniya daban daban saboda sun garkame kunnuwansu da abin sauraron waka da ake kira “head phones” hakan kan sa su manta da konai dakemkewaye dasu, basa jin karar mota da jirgin dake tafe a bayansu.
Irin wadannan ne matsalolin da yawan kamuwa da amfani da kafafen sadarwa zai iya kawo wag a rayuwar dan adam, irin wadannan matsalar kamar fadawa daga gada da wani ya yi, sun isa su zaburar damu don shi ga gangamin fadakar da jama’a a kan matsalar kamuwa da amfani da kafafaen sadarwa na zamani musamman a bangaren matasa.
A kwai misalai na kamuwa da hanyoyin sadarwa na zamani da dama, misali a halin yanzu da dan kudi kalilan zaka iya samar wa kanka da wakokin nishadantar da kanka, hakan kuma zai iya cutar da aikin da mutum yake yi, abun kuma da haifar da karancin aikin da mutane ke, tun farko kuma baa bin da ake fatan kimiyya da fasaha ya haifar wad a jama’a ba kenan.
Abin tambaya a halin yanzu shi ne wani mataki zamu dauka don rage matsalar yawan dogaro da ake yi a kan na’orurin sadarwa na zamani.
Daya daga cikin hanyoyin da zamu yi amfani dasu shi ne tsara yadda zamu gudanar da harkokin rayuwarmu nay au da kullum, mu kuma yi tsayin daka wajen amfani da abin da muka tsara. Kada dauki tsawon lokaci kana amfani da na’ura, ka samar wa kanka wasu abubuwan da zasu shagaltar da kai don su dauke tuaninka daga dadewa a kan na’ura.
Ya kamata ka kuma samar wad a kanka daidaito tsakanin harkokin da akke gudanarwa a cikin gida da kuma na waje, ka tsara wa kanka tsawon lokacin da zaka rinka amfani da na’urorin sadarwa ka kuma tabbatar da ka tsaya a kai sosai, haka zai taimaka maka nisantar na’uroron da kuma kamuwa da amfani dasu.
Ya kuma kamata ka rinka ba kanka hutu daga amfani da na’ororin, yin haka zai yi matukar taimakonka zai kuma taimaka wa kwakwalwaka ta rinka nunfasawa.
Ana kiran hada wadannan dabarun don samun kaucewa yawan dogaro ga na’urorin “digital detod,” wato tsawon lokacin da mutum ke yi wajen kautacewa amfani da na’uran zamani irinsu wayan hannu da kwamputa, ana kwatanta wannan lokaci a matsayin lokacin hutu da nisantar da kai daga matsalolin da amfani da wkadannan na’urorin ke haifarwa.
Wani hanyar rage dogaro da wadannan na’urorin ya hada da bayar da lokaci na musamman ga iyalanka da kuma shiga wasu harkoki kamar noma ko kuma yin bincike da nazarin tsaffin abubuwa, ma’ana a kwai bukatar ka shagaltar da kanka da wasu abubuwan da zasu dauke maka hankali daga ci gaba da dogaro da wayarka ta hannun da kwamputa da sauran na’urorin da kimiyya da fasaha sa kawo nama don saukake mana huldar rayuwa.
Wasu hanyar kuma ya hada da yin biris da sanarwar kana da sako da wayar hannun ke sanar da mai ita, ya zamana kana da lokaci na musamman da kake shiga social,miedia ba wai duk lokacin daka ji “notifications” sai kawai ka dauki waya ba, wadannan matakai nada matukar mahimmanci wajen taimaka don kuwa anyi amfani dasu koma an samu nasarar rage yawan dogaro ga waddan na’urorin. Yana kuma da kyau mu rage dogaro da na’urorin wajen warware wasu matsaloli kamar na lissafi da sauransu, mu lizimci amfani da kwakwalawarmu wajen fuskantar matsaloli, hakan zai taimakawa kwakwalwarmu da kuma rage dogaro ga na’ura. Gidauniyar “Goodwill Community Foundation,” ta tabbatar da cewa yawan dogaro ga kafafen sadarwa na zamani yana zama babban matsala, yayin da intanet ked a matukar amfani, yawan dogaro gare shi na haifar da matsala ga rayuwar dan adam.
Saboda haka yana da kyau a a yi kokarin hana yara kanana fadawa amfani da irin wadanna na’urorin tun suna kanana, musamman abin daya shafi wasannin kwaputa, ana iya sa musu doka na daina amfani da wadanna na’urori da zaran dare ya yi da kuma lokacin bacci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: