Khalid Idris Doya" />

Karuwar Korona: Gombe Ta Bukaci Jama’a Da Su Bi Dokokin Kariya

Ranar Yaki Da Kanjamau

Kwamitin yaki da cutar Korona a jihar Gombe ya yi gargadi ga al’umman jihar game da bin ka’idojin da matakan kariya daga cutar mai hanzarin illata mutane, a daidai gabar da da adadin masu mutuwa daga cutar ke karuwa.

Wannan kiranyen ya biyo bayan fuskantar bukukuwan kirisimeti ne da na sabuwar shekara tare kuma da lura da yadda cutar take kara bazuwa sannu a hankali.

Shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar a jihar Gombe Dakta Manasseh Daniel Jatau wanda shine mataimakin gwamnan jihar, ya shawarci al’ummar jihar da su bi ka’idojin kariyan kai daga cutar.

Dakta Jatau ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai game da sake barkewar cutar karo na biyu, yana mai cewa an gano karuwar adadin masu dauke da cutar dama masu mutuwa sanadiyyar ta a jihar.

Ya ce, “Sanin kowa ne gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ta yi duk abinda ya dace wajen dakile yaduwar cutar, amma lamarin ya sake barkewa karo na biyu tsakanin ‘yan Nijeriya”.

Ya ce zanga-zangar EndSARS da aka yi kwanakin baya a fadin kasar nan ma ya taimaka wajen yaduwar cutar ta korona.

Sai ya bukaci al’ummar jihar da su dauki dabi’ar bin ka’idojin gujewa yaduwar cutar da suka hada da sanya kyallen rufe hanci da baki da wanke hannu da barin tazara a tsakani.

“Mun kira ku ne, ku ‘yan jaridu don yi muku bayani kan ayyukan kwamitin tare da neman hadin kan ku don isar wa al’umma kan bukatar kowa ya bi kaidojin kare kai daga cutar Korona musamman ma a wannan lokaci na bukukuwa da tarukan shagulgula”.

Shi ma Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Ahmad Muhammad Gana ya bayyana cewa, cutar tafi kamari a wannan yanayin na sanyi.

“Abun da ba a son ji ne amma gaskiyar batun shi ne Jihar Gombe tana fuskantar barkewar cutar Korona da yawaitar mace-mace. Muna bukatar jama’a su san da hakan kana su dauki shawarorin da muke bayarwa domin kariya daga wannan lamarin.”

Daga nan Dr. Gana ya bukaci al’umma su bi ka’idojin kariya daga cutar, tare da gujewa karyata samuwar cutar.

 

Exit mobile version