Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Fadakarwa

Karya Da Cin Amana Da Saba Alkawari Da Tonon Asiri Da Rashin Koma Ma Allah  

by Muhammad
March 19, 2021
in Fadakarwa
7 min read
Allah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mahmud Sabo Wushishi

  1. Karya da cin amana da saba alkawari da tonon asiri da rashin komawa ga Allah, ko nisanta bawa ga Allah.
  2. Karya da cin amana suka jawo saba alkawari da tonon asiri da rashin komawa ga Allah, da nisantar bawa ga Allah.
  3. Karya da cin amana da saba alkawari ya kawo barin addini da kashe aure da saba wa makusanta ana tare an ki komawa ga Allah.
  4. Karya da cin amana da saba alkawari ya kawo rashin mafadi, ka ga mutum yana gaugawar yin abin da ya so bai duba Allah.
  5. Karya da cin amana da saba alkawari ke sa mace kwashe kaya da yin yaji ba umurnin iyaye, ba na Mallamai, ba batun Allah.
  6. Karya da cin amana da saba alkawari ya sa da ya bar uwa ko uba ya koma ga wanin su ya rabu da Allah.
  7. Karya da cin amana da saba alkawari ke sa barin wurin aiki da yin aikin da yin sana’a ba cinikayya babu bin Allah.
  8. Karya da cin amana da saba alkawari ya sa namiji sakin matarsa ko ita ta kwashen kayanta, iyaye suka sa ya ko ta sa kanta ba batun Allah.
  9. Karya da cin amana da saba alkawari ke kawo rashin mafadi a bi son zuciya ko ga mafadin amma mai saba ma Allah.
  10. Karya ita ce rashin gaskiya, cin amana kuma hada gaskiya da karya, saba alkawari barin su duka, ko ajiye guda a gurbin guda, iy ya koma a’a, a’a ya koma ey, an ki bin Allah.

BIN SON ZUCIYA DA RASHIN MAFADI NA KIRKI DUK DAYA:

  1. Bin son zuciya da rashin mafadi ko samun mafadi na banza a wurin mutum ko mutani duk daya.
  2. Bin son zuciya ya kawo cewa wani ko an ce wani ko wance na yin abu kaza mara kyawo, don ku zama daya.
  3. Bin son zuciya ya kawo an ce-an ce, in mutum ya ce ance wani ko wance na kaza mara kyawo ce masa ina ce kai ba ka yi ko? Kada ku zama daya.
  4. Bin son zuciyar mafadi, na son zuciyarsa, da bin son zuciyarka ko mai jinsi duk daya ne suke, in ka bi sai duka ku zama daya.
  5. Bin son zuciyar babba ko nagaba ya kawo bin nabaya, in nagaba bai gyara ba, ko nabaya da shi sai su zama daya.
  6. Bin son zuciya ya kawo yin gaban kai da kayan wani, ko kayan da ba kai ka fi hakki kansa ba, ko wanda kuke daya.
  7. Bin son zuciya ya kawo fifita wadanda ba su suka haife ka ba akan wadanda suka haife ka, ko ka fifita danwani ko diya.
  8. Bin son zuciya da rashin mafadi na kirki mai gaskiya, ya sa fifita Mallamin wani akan naka, ko ka mayar da su daya.
  9. Bin son zuciya ke sa iyaye watsi da ‘ya’yansu ko na kusa, su kama na wasu ko na nisa, ko da kawa darajansu daya.
  10. Bin son zuciya ya sa fifita buki don zumunta akan aure, amma ba bin son zuciya bane fifita aure akan zumunta ibadan mace mara aure na shekaru sittin bai na mai aure ba kwana daya.

FIFIKON NAMIJI AKAN MACE TUN DAGA ADAMU HAR TASHIN KIYAMA:

  1. Fifikon Adamu a kan Hauwa’u, tarihi ne ga ‘yan Adam na farko sai a biyo bayansa har tashin kiyama.
  2. Fifikon matar Ludu da na Nuhu na kafirci ne, masu gadonsu nanan na ta yi, na Maryamu da Asiya kuma na ibada nanan har tashin kiyama.
  3. Fifikon mafificin halitta Muhammadu (SAW) akan Khadija da Aisha akan mazajen kwarai nanan har zuwa tashin kiyama.
  4. Fifikonsa (SAW) akan Fatima na haihuwa, da na Sayyidina Abubakar akan Aisha, da Sayyidina Umar da Usmanu da Aliyu akan Sahabbai har tashin kiyama.
  5. Fifikon Sayyidina Aliyu akan Hassan da Hussaini (AS) na haihuwa nanan, na aure kuma akan Fatima har tashin kiyama.
  6. Fifikon miji akan mata da na iyaye akan ‘ya’ya dole ne, akan waninsu ne ba dole ba, darajar uwa akan da har tashin kiyama.
  7. Fifikon uwa akan da ko ubansa ba ya zama dole, domin akwai zabbabun bayin Allah, kamar Manzonmu har tashin kiyama.
  8. Fifikon Annabi Isa (AS) akan Maryamu (AS) uwarsa ce, ba’a daidaita su, darajar da Allah ya yi ma Isa akan nata har tashin kiyama.
  9. Fifikon Shaihu Usmanu na walitaka (RA) ya zarce na mahaifansa biyu, da na sauran iyaye da ‘ya’ya har tashin kiyama.
  10. Fifikon waliyyan Allah, a kowani bangare na duniya irinsu Shaihu Tijjani da Shehu Abdulkadiri ba’a tantama har zuwa yashin kiyama.

MATSALAR MUTUM NA KANSA SAI YA RIKA KALLONSA KAN WANI:

  1. Matsalar mutum da yawa na kansa ne, sai ya rika kallo akan wani, ko an gaya masa bai gani.
  2. Matsala na kan mutum ana gani, amma shi ba ya gani kuma ko ya shafa ba ya ji, sai mai tunani.
  3. Matsala ce babba ka daidaita kanka da mai yinka, mai tafi da rayuwarka, kuma kai ka kafe ba ji ba gani.
  4. Matsalar ka ka kwashe duka ka dora wa makusanta ko mutani, koma kowa kamarka yake ko ba ya ji ba ya gani.
  5. Matsalar marayu da mai iyaye sa’a ce kawai daga Allah, wani marayar ba’a finsa jindadi kuma babu jin ko ba gani.
  6. Matsalar wani ga iyayen sun kasa cisshe shi ko ita wani ke dauke da jan takalisunsu har iyayen suna ji suna gani.
  7. Matsalar mutum ba ta wuce rashin sanin Allah ba, da tsarin da ManzonSa ya bar mana, ba’a ji ba’a gani.
  8. Matsalar rayuwa yau duka ta koma ne ga lauyoyi, kokuma ka ja baya da ci-gaban duniya, kana ji kana gani.
  9. Matsalar wanda aka cuta sai ga lauya, mai cutarwa ma ga lauya, shi mai sharia alkali ga lauya ba ji ba gani.
  10. Matsalar addini ga lauya, na kusa ma ga lauya, na auratayya ga lauya, iyaye da ‘y’ya ma ga lauya ana gani.
  11. Matsalar siyasa ga lauya, filaye ciniki aiki sana’a kiwon lafiya da tsoronta lauya, in ba lauya ba ji ba gani.

KARANCIN SANI DANA BINCIKE DA NA SHEKARU MATSALOLI NE:

  1. Karancin sani dana bincike da na shekaru matsaloli ne, ga duk mai hankali, ba wanda za ya ce dayan su ko biyunsu ko dukansu wurinsa ba matsala bane.
  2. Karancin sani ya kawo jiran lokacin buki, har ya hana zuwa gayar da mara lafiya, amma jiran lokacin buki in an sa rana yana iya jirkita gaisuwar mutuwa in nisa ne.
  3. Karancin sani ya sa ake daidaita yin aure da daukan takalifunsa, daukan takalifun aure ya fi na yin auren, yin aure sunna ce, daukan takalifunsa farilla in an gane.
  4. Karancin sani da na shekaru da na bincike matsala ce ga mutum, aure na zama tilas in ana tsoron zina, kuma akwai halin daukan takalifunsa ga wanda ya gane.
  5. Karancin sani ya sa mutum fadawa cikin aikin haram da zaton sunna ko tilas, ya ce wajibi ne a kansa, aure in ba daukan takalifunsa, dawainiyarsa ga mata ko miji ake nufi bayan an daura shi ne.
  6. Karancin sani da rashin bincike da karancin shekaru, kan sa mutum aure alhali yin sa haramune akan ma’aura ko dayansu, in ba yin zina kuma ba abin bukata ga kowanne.
  7. Karancin sani yasa aka kasa gane aure na zama halal ko abin so, ga wanda ba ya tunanen yin zina, kuma yana iya daukan takalifun kansa ko na gudansu in rikon sunna ce.
  8. Karancin sani yasa aka kasa gane aure na zama tilas ga wanda zai yi zina in bai yi ba, maco ko namiji, amma in da auren zai bari, sai a taimaka ayi auren ya fi, ko da daukan takalifun zai kai ga cin haram in ba zai hada da kisa bane.

AN KI CIN BIRI AN CI DILA:

  1. An ki cin biri an ci dila, ka ki bin son zuciyarka ka bi ta wani ba Allah ba, ba’a rabu da bukar ba, an haifi Abu, ba’a so balarabe ba, amma ana son bala.
  2. An ki a raba kasa, amma an yi mata jaha-jaha, an ki a raba jaha amma an yi mata kananan hukumomi a karamar hukuma an yi mazaba an yi yankin kansila.
  3. An ki raba gari mai masarauta daya, amma an yi unguwa-unguwa da masu unguwanni, a unguwa daya ga gidaje daban-daban, don kada a hade a sami matsala.
  4. An ki yin zauruka a gida daya, sai zaure daya ba’a yi ma kowani shiya zaurensa ba, kowani shiya kuma kowa da dakinsa ko nasu don gudun wahala.
  5. An ki raba tukunya a daki daya ko shiya daya, sai in ya zama dole, amma in an yi tukunya daya kowa da kwanunsa ko nasu, kuma akan yi ma kowa malmala.
  6. An ki gaskiya dole sai karya za’a kama, abin da ya hada kasa daya, ba shine ke hada jaha ba, abin da ya hada jaha ba shine kan raba hukumomi ba in an kula.
  7. An ki bin addinin wani ga wani nason ya bi shi, ana son tankwara ga bin abin da ba nasu ne a gidansu ko a garinsu ko jaharsu ko kasarsu ba, ana yin kutungwila.
  8. An ki bin al’adun wasu, masu shi na son abin su, ana kawa masu na wasu ko ana son su bi, su bar nasu, an ce kowa na da ‘yancin nasa; “mai kwadayi idonsa da kulu, ba ya ga nasa yana ta harara zai ta hawaye bayan kwalla.

KWADAYI MABUDIN WAHALA DA YAWAN HASARORI:

  1. Kwadayin dan’arewa na samun dukiya da tara ma kansa ko nasa, wanda ke iya ja masa ya ja ma yankinsa ko kasarsa wahaloli da yawan hasarori.
  2. Kwadayin dan’arewa ne ya sa sauran yankunan kasa ta, kuma kasarmu Najeriya, ke son su balle su bar ta, a can baya ba inda suke so kamar arewa a boye har a sarari.
  3. Kwadayin dan’arewa da son tara kudi da son girma ko daukaka da sauri ba tare da bin hanyar da zai same su ba, sai yana fadawa ga kaskancin yaro karami jinjiri.
  4. Kwadayin dan’arewa akan abin wani da abinda bai kai ya mallake su ba, bance arewa duka ba, yau ya jefa mu har shi da nashi ko ita, ko ta’ina cikin garari.
  5. Kwadayin dan’arewa akan abin wani ko matsayin da yake son ya kai ko ta kai cikin hanzari a rayuwar duniya ke jefa wasu shugabannimmu da makusantansu na kwarai cikin hadari.
  6. Kwadayin dan’arewa mafi yawan mazammu da mata sun mance Allah da lahira da sanin duniya suke, ba cikin aljannan da lahirar da addinimma kamar sun bari.
  7. Kwadayin dan’arewa yau ya kai ga in kana jawo hankalinsa akan abin duniya, sai ya ce maka waye ba ya so, tun ba kudi ba, son tara su ake tsoro cikin kabari.
  8. Kwadayin dan’arewa da son tara kudi da mulki da tara iyali a bar su, ke jefa kowa cikin matsala, na saman da na kasan mai shi da mara shi, mai neman duniya kamar ba zai mutu ba, mai son lahira kamar yanzu za’a sashi kabari.

Wushishi ya rubuto daga Bosso, Jihar Neja

08055736329 08034358678

 

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Tarukan NPC Da NPPCC Na Kasar Sin Na Da Muhimmanci Sosai Ga Ci Gaban Kasar

Next Post

Yau Ake Raba Jadawalin Kofin Zakarun Turai

RelatedPosts

Hadisai

Hadisai 100 Daga Manzon Allah (S) A Kan Batutuwa Mabambanta

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Marazu Hasan D/Sure,Roni, 07031615160. Wadannan wadansu Hadisai ne da...

Kame Kai Daga Abubuwan Da Ba Su Dace Ba Ga Mai Azumi

by Muhammad
3 days ago
0

Da farko muna gode wa Allah mai rahama mai jinkai...

Lura

Abu Uku A Kan Mutun Uku Ababen Lura

by Muhammad
1 month ago
0

Daga Mahmud Sabo Wushishi, Abu uku dole ga malami ko...

Next Post
Turai

Yau Ake Raba Jadawalin Kofin Zakarun Turai

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version