Abubakar Abba" />

Kasafin 2019: Cibiyar CSJ Ta Shawarci Buhari Kan Dakile Barakar Kudin Shiga

Cibiyar dake fafutukar tabbatar da adalci CSJ, ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da dauki matakai a bayyane don dakile barakar fitar kudin shiga na kasar nan daga daukacin hukumomin Gwamnatin Tatarayya ba a bisa ka’ida ba.    

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ne ya bayar da wannan shawarar a martanin sa akan rattaba hannun da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi akan kasafin kudin shekarar 2019.

Idan za a iya yunawa, a ranar Litinin data gaba ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannun akan kasafin kudin na shekarar 2019 ya zamo doka.

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya yi nuni da cewa, rattaba hannun da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi akan kasafin kudin na shekarar 2019 abune na ci gaba ga kasar nan.

Sai dai, Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya ya ankarar da cewar, amincewa da kasafin a makare  da rattaba hannun akan kasafin kudin na shekarar 2019, anyi a makare, wanda kamata ya yi ayi a cikin watan Janairun    shekarar 2019, idan akayi la”akari da matsalar da tattalin arzikin kasar nan yake a ciki a halin yanzu.

A cewar Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya jinjinawa bangaren zartarwa na yin hanzarin tura kudi don wanzar da kasafin kudin na shekarar 2019.

A cewar Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere, akwai bukatar GwamnatinnTarayya a yanzu ta fara mayar da hankali na shirye-shiryen tsara kasafin shekarar 2020.

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere, dole ne Gwamnatin Tarayya ta dauki matakai  wajen kaucewa shirya kasafin kudi a makare gabatar dashi da kuma aminceea dashi, musamman don a gudanar da shirye-shiryen tsara kasafin kudi na shekarar 2020 mai zuwa don gabatarwa a gaban yan Majalisar Kasa a cikkn watan Satumbar shekarar 2019.

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya yi nuni da cewar, akawai matukar bukatar Gwamnatin Tarayya ta dauki dukkan matakan da suma dace don inganta wanzar da zaman lafiya da kuma kara jan alummar yankin Neja Delta mai albarkar man fetur, yadda za’a samu sukunin kara yawan man fetur da ake sarrafawa din ya kai bukatar da ake dashi ta yawa mbpd 2.3.

A cewar  Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere, ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta dauki dukkan matakan da suka dace don dakile dukkan wata baraka a daukacin hukumomin ta don kare fitar kudin shigar ta.

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya kuma yi nuni da cewa, akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta  sabunta yadda ake rabar da kwangilolin sarrafa man fetur kamar yadda Hukumar Cibiyar Nazari ta Masana’antu NEITI.

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya yi nuni da cewar, hakan kara samarwa da Gwamnatin Tarayya nudin shiga kasa da dala biliyan 1.6 ako wacce shekara.

Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere yaci gaba da cewa,“turwa da sanya hannu akan kudurin fannin man fetur PIB yadda za’a samu sukunin inganta fannin mai da iskar in  gas da kuma kara samarwa da Gwamnatin Tarayya kudin shiga na ribar da aka samu daga fannin na man da iskar gas.

A cewar Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere ya yi nuni da cewa, akwai bukatar majalisar Kasa  su fara yin aiki akan kudurin na PIB.

Cif Eze Onyekpere yace, Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwaiwar da Majalisar ta Kasa don daukar matakan rage tsadar wanzar da aikin gwamnati.

A karshe Daraktan Cibiyar ta CSJ Cif Eze Onyekpere yace, Ministan Kudi na kasar suci gaba da tabbatar da bin ka’ida ta FRA.

Ayyukan da kuma karfin iko dake a karkashin FRA da mahukuntan kudi a bisa doka.

Exit mobile version