’Yan Nijeriya su shirya jin sabon karin radadi a cikin kasafin kudin shekarar 2021, kamar yadda ministar kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa, Misis Zainab Shamsuna Ahmed da shugaban ofishin kasafin kudi na tarayya, Mista Ben Akubueze suka bayyana wajen bayanan kasafin kudin shekarar 2021 na tiriliyan 13.588 na kasafin kudin gwamnatin tarayya.
Manyan ma’aikatan fadar shugaban kasa sun kara jaddada cewa, an cire tallafin wutar lantarki gaba daya a Nijeriya a cikin shirin kasafin kudin gwamnatin tarayya na wannan shekara, haka kuma a dai-dai lokacin da ake kayyade farashin mai a kasuwan duniya, ‘yan Nijeriya su shirya fuskantar tsadar mai duk da kasar tana daga cikin manyan kasashe masu samar da mai. Sun kara da cewa, haka ma a fuskanta a bangaren wutar lantarki wanda aka kara kashi 50 a ranar 1 ga watan Junairu.
Sun bayyana cewa, suna tattaunawa da masanan tattalin arziki a cikin shirin kasafin kudin na gwamnati ta yadda za a samu wa ‘yan Nijeriya sauki.
Da yake jawabi a kan goyan bayan cire tallafi, farfeso a harkokin kudade da ke jami’ar Jihar Nasarawa, Uche Uwaleke ya bayyana cewa, wannan shi ne hanya mafi mahimmanci da zai amfani talaka.
A yanzu gwamnatin za ta iya amfani da wadannan kudade na tallafi wajen bunkasa mahimman fannoni, kamar yadda tsohon shugaban cibiyar bincike tattalin arziki, Farfesa Olu Ajakaiye ya bayyana, wanda ce wannan ne shirin da gwamnati za ta yi wajen yaki da talauci. Ajakaiye ya ci gaba da bayyana cewa, cire tallafin zai sa hauhawar farashin kayayyaki wanda hakan zai haifar wa talaka mummunan rayuwa.