Yusuf Shuaibu" />

Kasafin 2021: Buhari Da Osinbajo Za Su Ci Abinci Da Balaguron Naira Biliyan N3.4

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo za su kashe naira biliyan 3.4 wajen abinci da tafie-tafiye. An warewa ofishin shugaban kasa Buhari naira biliyan 2.6, yayin da aka warewa ofishin Osinbajo naira 873. A shekarar biyar da suka gabata, kudaden tafiye-tafiye yana sanadiyya kashe kudade masu yawa a cikin kasafin kudi. Yawan kudaden daya ne da aka kashe a shekarar 2020 ga wadannan ofisoshi gudaa biyu a cikin kasafin kudi. Haka kuma ana kashe kudade masu yawa wajen ciyarwa ga wadannan ke cikin wadannan ofisoshi guda biyu.

Tafie-tafiye da ciyarwa ya lakume naira biliyan 1.5 a shekarar 2019, haka kuma an kashe naira biliyan 1.52 a shekarar 2018, an narkar da naira biliyan 1.45 a shekarar 2017, sannan an kashe naira biliyan 1.43 a shekarar 2016. Fadar shugaban kasa zai cinye naira biliyan 2.4 wajen tafiye-tafiyen, inda tafiye-tafiye cikin gida Nijeriya zai ci naira miliayan 775.6, yayin da tafiye-tafiyen kasashen ketare zai cinye naira biliyan 1.7.
A bangare daya kuma, mataimakin shugaban kasa Mista Osinbajo zai kashe naira miliyan 801 wajen tafiye-tafiye a shekara, inda tafiye-tafiyeb cikin gida zai ci naira miliyan 284, yayin da tafiye-tafiyen kasashen ketare zai ci naira miliyan 517.1.
Haka kuma, yawan kudaden da za a kashe wajen ciyar da shugaban kasa Buhari da mataimakinsa Osinbajo ya kai na naira miliyan 194.5. Wanda iyalai na farko za su ci kudade na naira miliyan 124. Wannan yawan kudade dai-dai yake da wanda aka amince wa shugaban a cikin kasafin kudi na shekarar da ta gabata. A cikin naira miliyan 124 wanda aka amince a kasafin kudin wannan shekarar, kayayyakin abinci zai ci naira miliyan 98.3, yayin da kayayyakin shaye-shaye zai su ci naira miliyan 25.7.
Iyalan na biyu kuma za a ciyar da su kamar yadda aka yi na shekarar ukun da ta gabata na naira miliyan 71.5 a wannan shekarar. Wannan ya nuna cewa, an samu ragi daga naira miliyan 88.9 wanda aka kashe a shekarar 2018, amma kuma an samu kari a kan na shekarar 2017 na naira miliyan 53.7 da kuma na shekarar 2016 wanda aka kashe naira miliyan 24. Za a kashe naira miliyan 50.9 wajen sayan kayayyakin abinci, yayin da kayayyakin shaye-shaye zai ci naira miliyan 18.3, inda gas na girki da man fetur za su ci naira miliyan 2.4.

Exit mobile version