Daga Umar Faruk
Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya gabatar da Naira Biliyan 141,644,270,119 a matsayin kudirin kasafin kudi na shekar ta 2021 na jihar ta kebbi a jiya a Birnin-Kebbi ga majalisar dokokin jihar.
Kasafin kudin dai da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya gabatar a majalisar ta dokokin jihar zai bada muhimmacin ga harakokin ilimi, kiwon Lafiya, Aikin Gona, samar da ruwan sha da kuma tsarin samar watasa ayyukkan yi.
Sauran sun hada da bukasa kannan hukumomin, tsaro a duk fadin jihar ta kebbi da kuma ayyukkan gine-gine a Babban Birnin jihar da kuma fadin kananan hukumomin Ashirin da daya jihar ta kebbi. Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da kafin kudin ne a gaban majalisar ta dokokin jihar a jiya .
Hakazalika Gwaman Abubakar Atiku Bagudu ya kara da cewa” gwamnatinsa ta shirya kasafin kudin shekara ta 2021 ne bisa yanayin tattalin arziki kasar Nijeriya da kuma na jihar ta kebbi domin gwamnatin jihar ta iya cinma bukatunta da kuma na mutanen da take mulki a jihar, inji shi”.
Bugu da kari ya ce” duk da hakan jahohin kasar nan na fuskanta kalubale domin ko a kwanan jahohin kasar nan sun fuskanci barazanar zanga-zanga ga wasu matasan kasar har wasu suka rika balle wuraren gwamnatin da na ‘yan kasuwa suna kwashe kaya da kuma samun matsaloli tare da jami’an ‘yan sandan kasar Nijeriya ta suke yiwa taken (endSARS), wanda an samu asarar dukiyoyi da kuma rayukku a wasu jahohin kasar nan, wanda matsalace ga tattalin arzikin kasa.
Har ilayau ya ce” wannan abinda matasan kasar Nijeriya su kayi ya nuna cewa akwai bukatar shuwugabannin kasar nan su kara inganta ayyukkan shugabancinsu da kuma mu’amilarsu da mutanensu, inji Gwamna Abubakar Atiku Bagudu a majalisar dokoki ta jihar kebbi yayin da yake gabatar da jawabinsa na cikin kasafin kudi na shekara ta 2021″.
Daga karshe Gwamna Bagudu ya godewa majalisar dokoki ta jihar kebbi kan bashi damar gabatar da kasafin kudi na shekara ta 2021 a gaban ta. Ya kuma yabawa shuwugabannin da mambobbin majalisar kan irin hadin kai da suke bawai majalisar zartarwa ta jihar kebbi a karkashin jagorancinsa wurin tabbatar da cewa al’ummar jihar sun ci gajiyar mulkin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu.