Daga Khalid Idris Doya
Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun nuna takaicinsu da karancin kudaden gudanar da manyan ayyuka a shiyyar da aka ware a kasafin kudin 2021, su na masu neman majalisar kasa da ta sake waiwaye gami da nazarin kasafin domin tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin shiyyoyin kasar nan.
Jawabin bayan taron da suka fitar na cewa: “Kungiyar ta bayyana takaici ganin duk da irin kalubalen ci gaba musamman a fannonin ayyukan raya kasa da shiyyar ke fuskanta, Naira biliyan 45.32 ne kacal aka ware don manyan ayyuka wa yankin a kiyasin kasafin kudin badi. Wanda hakan bai wuce kaso 0.035 cikin dari ba na kasafin kudin, wanda ya kai Naira triliyan 13.02. Wannan na nufin an yi watsi da shiyyar Arewa Maso Gabas.”
Don haka kungiyar ke kira ga majalisun tarayya su sake dubi kan kasafin kudin na badi don tabbatar da daidaito da tafiya da kowa. Ta kuma bayyana goyon baya ga ‘yan majalisun wakilai da na dattijan dake wakiktan shiyyar su dauki matakan gaggawa na ganin an yi gyara ga wannan rashin daidaito.
Kungiyar ta kuma koka kan rashin adalcin da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya ke yi ta fuskar samar da hanyoyin mota. Ta kuma bayyana takaicin yadda ayyukan hanyoyin da aka bayar a yankin ke tafiyar hawainiya ko ma suka tsaya cak, inda ta yi kiran a gaggauta sake dubi kan halin ni ‘yasun da kwangilolin da aka bayar a yankin suke ciki.
Kungiyar gwamnoni Arewa Maso Gabas da ta kunshi gwamnonin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe, sun tattauna ne kan kalubalen da shiyyar ke fuskanta da kuma daukan matakan da suke ganin za a samu shawo kan wasu daga cikin matsalolin.
Kan lamarin tsaro a shiyyar, Kungiyar gwamnonin ta lura cewa ana samun ci gaba a sha’anin tsaro a yankin. Amma duk da haka, aika-aikar ‘yan kungiyar Boko Haram da na ‘yan bindiga, da barayin shanu da masu garkuwa da mutane na ci gaba da zama barazana ga ci gaba mai dorewa a yankin.
Duk da gwamnonin sun yaba wa kokarin jami’an tsaro a shiyyar, ta amince ta karfafa ‘yan sandan cikin al’umma tare da dafawa kokarinsu, kana sun nemi jami’an tsaron su kara himma domin karasa kakkabe ‘yan ta’adda a yankin.
Kungiyar ta kalailaice irin kalubalen da ilimi ke fuskanta a shiyyar, inda ta yanke shawarar tinkarar matsalar a kungiyance don farfado da sashin, musamman ma ilimin firamare, inda ta yanke shawarar kirkiro hukumar kula da ilimi ta shiyyar arewa maso gabas.
Kungiyar gwamnonin ta kuma jaddada himmatuwar ko wace jiha a shiyyar wajen karfafa dokar ilimin bai daya daga tushe ta UBEC don tabbatar da cewa daukacin yaran yankin sun samu damar samun ilimi daga tushe.
“Kungiyar ta bayyana bukatar karfafa hada karfi da karfe tsakanin jihohin shiyyar don tinkarar matsaloli da bukatun da za su amfani jihohin yankin, inda gwamnonin yankin suka amince su nada mashawarta na musamman kan sha’anin karfafa alaƙa tsakanin jihohin shiyyar.”
Jawabin matsayar bayan taron na kuma nuni da cewa, kungiyar ta nazarci batun kudin tallafin farfado da tattalin arziki bayan illar da annobar Korona ta janyo, wadanda suka kai Naira triliyan 2.3. yaayin da take jinjinawa gwamnatin tarayya bisa kirkiro da wannan tsari, ta bukaci a tabbatar da adalci da daidaito wajen rabon tallafin, musamman bisa la’akari da kalubalen tattalin arziki da zamanta kewa dake addabar yankin.
Daga bisani karshen taron ya cimma matsayar cewa taron da za ta gudanar a nan gaba zai guda ne a tsakanin ranakun 3 da 4 ga watan Maris na badi a jihar Bauchin Yakub