Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Emmanuel Bwacha, ya soki Shugabannin Nijeriya karkashin jagorancin Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kan rashin kebewa fannin aikin noman kasar nan isassun kudade.
Emmanuel Bwacha ya yi sukar ce lokacin da Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono, ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan harkar noma don kare kasafin kudin ma’aikatar na 2021.
Kasafin kudin, wanda aka aike wa da majalisar kasa, yana jiran ‘yan majalisar su amince har ila yau, kasafin kudin da aka gabatar wa bangaren, kasa da kashi biyu cikin 100 na kasafin kudin 2021, ya sabawa da yarjejeniyar taron harkar noma na Afrika da ake kira taron Maputo.
A shekarar 2003, Nijeriya na daga cikin kasashen da suka shiga yarjejeniyar ta Maputo wacce ta umarci dukkan kasashe yayan kungiyar su kebe akalla kashi 10 na kasafin kudinta na shekara-shekara ga harkar noma.
Yarjejeniyar takunshi muhimman shawarwari da dama, daga cikinsu akwai jajircewar akalla kebe kashi 10 na kasafin kudin kasa ga harkar noma da ci gaban karkara a cikin shekaru biyar.
Sai dai, tun lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, Nijeriya ba ta taba cimma burin da aka sa gaba na kebewa fannin noma da kudade masu ya wa ba.
Mista Bwacha ya so ki shugabannin yanzu da na baya game da cin amanar da yankin ta hanyar talaucin kudaden da aka kebewa, inda ya kara da cewa, mun gaza saboda wannan bayanin da aka yi a karkashin Tarayyar Afirka wacce kuma an yi ta ne a karkashin gwamnatocin kasashen da suka shiga yarjejeniyar.
Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Emmanuel Bwacha, ya kara da cewa, ba ma a kasafin kudi na kasa daya ba mun kuma iya daukar kashi 7 cikin dari.
Ministan Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Na Nono wanda ke kan kujerar shugabancin Bankin Raya Kasashen Afirka ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya suna ta fa ta sosai kan ci gaban fannin noman kasar nan, inda ya kara da cewa, an yinkokari don wayar da kanmu game da fadada tattalin arziki.
A cewar Ministan Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono, na damu saboda wasu mutane sun dora laifin kan gwamnatin daga 1999 har zuwa yau, inda ya kara da cewa, na ambaci hakan ne saboda dukkan shugabanin da ministocin da da suka yi aiki tsawon shekaru ba su iya nuna kwazo na gaske ba saboda ana zuba kudin a bangaren noma.
Ministan Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Sabo Nanono ya kara da cewa, yaushe ne za mu dauki wannan da muhimmanci watakila a matsayin al’umma ko a matsayin majalisa, tare da zartarwa.