Inganta tsarin ilimi da kiwon lafiya su ne abubuwa mafi muhimmanci a kowace kasa, kuma hakan ya faru ne saboda daukakar matsayin su ga rayuwar dan Adam; babu kasa ko al’ummar da ta ci gaba ba tare da hawa kan tsanin ilimi ba hadi da lafiya uwar jiki. Bugu da kari, ta dalilin muhimmancin su ne ya jawo ta kan su ake fara auna ci gaban kowace kasa ko akasin hakan. Amma me ya faru a tarayyar Nijeriya?
Me ya sa kullum ana ta famar kai ruwa rana tsakanin kungiyar malaman jami’o’i ta ASSU da gwamnatin tarayya? Sannan ga matsaloli kala-kala a fannin ilimi; ma su alaka da karancin jarin da gwamnayin tarayya ke zubawa tsarin gudanar dashi. Kana kuma kowanen mu shaida ne dangane da bullar annobar korona a duniya, cutar da ta zama alakakai a wasu manyan kasashen da su ka dade a sahun farko a ci gaba, balle kuma yan ku-ci-ku-bamu?
Wanda ko saboda wadannan dalilan da makamantan su; a bar zancen cutukan da su ka samu gindin zama, ya dace gwamnatin tarayya ta fi mayar da muhimmanci a kasafin kudin da take gabatarwa a kowace shekara kan ilimi da kiwon lafiya fiye da kowane bangare. Sai dai idan akwai abinda ya fi so muhimmancin, wanda a hakikanin gaskiya da damar yan Nijiriya ba su san shi ba!
Ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa kudurin kasafin kudin 2021; naira tiriliyan 13.08 zuwa doka, wanda majalisun dokokin tarayyar Nijeriya su ka bi diddigi tare da yi masa kwaskwarimar kari zuwa tiriliyan 13.6 kafin sun amince dashi.
Duk da manyan kalubalen da harkar ilimi a Nijeriya ke fuskanta tare da kiraye-kirayen da kwararru da korafe-korafen da yan kasa ke yi kan bunkasa harkokin ilimi, amma bai hana shugaba Buhari ware wa fannin kaso 5.6 cikin dari a adadin kasafin wanda shi ne kaso mafi karanci cikin shekaru 10 da su ka gabata a kan ilimi.
Hakan ya nuna ma’aikatar ilimin tarayyar Nijeriya an ware mata biliyan 77.6 wajen gudanar da harkar ilimin bai-daya, wanda ya hada makarantun furamari da sakandire da ke karkashin kulawar gwamnatin tarayya, sauran abinda ya rage kuma a karkasa shi zuwa manyan makarantu da cibiyoyin ilimi a fadin Nijeriya.
Nijeriya ta yi kaurin suna wajen yi wa harkar ilimi kauro da nuna masa shakulatin bangaro, matakin kasa ga yadda hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta kayyade cewa kar ya yi kasa ga kaso 15 zuwa 20 na kasafin kowace shekara a kasashen duniya.
A cikin wani rahoton da UNESCO ta fitar a 2018, mai taken: Ilimi domin ci gaban kowa tsakanin 2000-2015- nasarori da kalubale. Ya nuna yadda aka cimma matsaya tsakanin kasashen duniya kan hakan wajen bunkasa harkokin ilimin.
Har wala yau, a shekaru 10 da su ka gabata, kaso mafi tsoka wanda harkar ilimi a Nijeriya ta taba samu shi ne kaso 10.7 cikin dari a 2015 wanda gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gabatar a 2014. Wanda tun daga wannan lokadin, ba a sake samun makamancin sa ba.
A 2011, bangaren ilimin ya tashi da kaso 9.3 a kasafin shekarar wanda ya yi daidai da naira biliyan 393.8 inda daga baya aka aiwatar da kaso 9.86; naira 468.3 a kasafin, sai a 2012 an ware wa fannin biliyan 499.7 kaso 10.1 cikin dari, sai 2013 biliyan 494.7- kaso 10.5, da 2014 biliyan 484.2 da kaso 10.7 a 2015.
A 2016, ya fara rikitowa kasa inda ya samu naira biliyan 369. 6 daidai da laso 7.9 cikin dari na kasafin kudin, da jimlar biliyan 550. 5 a 2017, daidai da kaso 7.4, naira biliyan 605.8 a 2018 kimanin kaso 7.04; sai biliyan 620.5, kaso 7.05 a 2019, sai naira biliyan 671. 07 daidai da kaso 6.7 a 2020.
Wanda hakan ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta ware naira 2, 735 wajen kula da lafiyar kowane dan Nijeriya daya a shekara; kimanin mutum miliyan 200.
Bugu da kari, wannan jimlar kudin da aka ware wa harkokin kiwon lafiya ya kumshi biyan albashin ma’aikata da sauran abubuwan da ma’aikatar ke da bukata yau da kullum- baki dayan manya da kananan cibiyoyin kiwon lafiya a fadin kasar nan.