Kasancewar Mutane Masu Akidu Da Al’adu Daban-Daban Na Bukatar Hakuri Da Mutunta Juna
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasancewar Mutane Masu Akidu Da Al’adu Daban-Daban Na Bukatar Hakuri Da Mutunta Juna

bySulaiman
3 years ago
Hakuri

Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da wani taro a jiya, albarkacin ranar adawa da kalaman kiyayya ta duniya, inda zaunannen wakilin Sin dake majalisar Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya su mutunta tare da hakuri da juna, kana su rika tattaunawa cikin adalci don yaki da kalaman kiyayya.

Kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka gabatar da kudurin ayyana ranar ta yaki da kalaman kiyayya a shekarar 2021, inda aka fara gudanar da ita karon farko a bana.

  • Xi Ya Yi Kira A Hada Gwiwa Don Yaki Da Rashawa

Kamar yadda wakilin na Sin ya bayyana, yaki da kalaman kiyayya na bukatar kasashe su mutunta ’yanci da moriyar juna, da watsi da girman kai. Matukar da gaske ana son cimma zaman lafiya a duniya, to ya kamata gwamnati ta zama abar koyi ga jama’arta.

Bai dace gwamnati ta rika yada karairayi da zarge-zarge ba, domin jama’arta za su yi koyi da ita, lamarin da zai haifar da gadon kiyayya mara tushe tsakanin al’ummomi. Misali, an ga yadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya rika danganta annobar COVID-19 da kasar Sin, lamarin da ya sa aka rika nuna kyama ga mutanen Sin da Asiya a kasar da sauran kasashen yamma. Ko a lokacin babban zaben kasar, irin furucinsa ne ya haifar da harin da magoya bayansa suka kai ginin majalisa ta Capitol a kasar.

Hakuri shi ne tushen zaman lafiya. Kasancewar mutane daban-daban, masu addinai da akidu da launi da al’adu daban-daban, na bukatar hakuri da mutunta juna. Hadin kan kasa da kasa don moriyar juna, cikin adalci da mutunta juna, zai iya tabbatar da zaman lafiyar da ake muradi.

Haka zalika shirye-shirye kamar irin na abota tsakanin matasan Sin da Afrika dake zaman dandalin musaya, zai yi gagarumin tasiri wajen kawar da rashin fahimtar dake haifar da kiyayya.

A ganina, nan gaba, matasan Sin da Afrika da za su zama manyan gobe, za su kasance tamkar ’yan uwa ba tare da la’akari da bamban-bambacen dake tsakaninsu ba.

Irin wannan shiri da makamantansa, za su kawar da kyama da kiyayya don tabbatar da zaman lafiya da mutunci da kuma jituwa tsakanin al’ummomi. Wannan, shiri ne da ya kamata sauran kasashe su yi koyi da shi yayin da ake kokarin kawar da kiyayya a duniya. (Fa’iza Muhammad Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
Hajjin Bana: NCAA Ta Ziyarci Filin Jirgin Gombe, Ta Ce Filin Zai Yi Jigilar Alhazai

Hajjin Bana: NCAA Ta Ziyarci Filin Jirgin Gombe, Ta Ce Filin Zai Yi Jigilar Alhazai

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version