Connect with us

LABARAI

Kasar Afrika Ta Kudu Ta Halasta Shan Wiwi

Published

on

Wata kotun tsarin mulki ta Afirka ta kudu ta halatta shan tabar wui wui ranar Talata.

Shi wannan yanke hukuncin ya samu ne bayan da babbar kotun, a shekarar  2017 ta gano cewar, yin amfani da da tabar wiwi, a wani wuri daban, ya kamata a rika shan tabar, saboda dokokin da suke nuka akwai matsala, da tsarin mulki na kasa.

Ita gwamanati ta daukaka karar zuwa kotun tsarin mulki wanda ta amince da hukuncin babbar kotun tayi.

“Yanzu ya kasance ba laifi bane akan wani babban mutum ya mallaki hankalin shi, ya yi amfani da tabar wiwi, ko kuma ya aje ta a wwani wuri ko kuma gidan shi, mai shari’a Alkali Raymond Zondo, ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da hukunci.”

Shi yanke wannan hukuncin bai yi wani bayani ba.

Sai dai kuma shi yanke hukuncin bai yi wani bayani ba ko wacce irin wuiwi wato kadan ko kuma mai yawa, wadda za a iya ajiyewa gida domin amfanin wani.

Ana dai tayin murna da yanke wannan hukuncin a kotun , wadda  mashayen tabar da suka cika kotun da kuma wadanda suke goyon bayan mashayan tabar ta wiwi, da kuma mabobin al’ummar Rastafarian na Afirka.

“Al’amari ya kasance ne koda wanne lokaci ana yi ma ‘yan Rastafariya cin mutunci” cewar wani daga cikin wadanda suke murna da dokar data bada dama a sha wiwi ko kuma a aje ta, Prince kamar yadda yak afar yada labarai ta TB Channel e NCA.

 
Advertisement

labarai