Kasar Jamus ta doke kasashen Turkiya da Belgium a fafutukarsu ta neman izinin karbar bakwancin gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta shekara ta 2024, wato EURO 2024 bayan kwamitin gudanarwar hukumar ya kada kuri’a.
An gudanar da zaman kada kuri’ar ne a birnin Nyon na kasar Switzerland a ranar Asabar bayan kasashen biyu sun gabatar da yunkurinsu na karshe kan batun.
A karon farko kenan da Jamus za ta gudanar da wannan gasar tun bayan hadewarta da Jamus ta Yamma wadda ta karbi bakwancin gasar a shekarar 1988.
Kawo yanzu, Turkiya ba ta samu damar daukan nauyin wata babbar gasar kwallon kafa ba duk da kokarin da ta yi a shekarun 2008 da 2012 da 2016 na ganin ta karbi bakwancin gasar ta Turai.
Ita ma kasar Belgium bata samu damar ba wanda hakan yake nufin sai dai su sake shiryawa nan gaba domin samun damar daukar gasar wadda itace gasa mafi girma ta kasashe a nahiyar turai.
Kasar Faransa ce dai ta kabi bakuncin gasar da aka buga a shekara ta 2016 kuma taje wasan karshe sai dai tayi nasara a hannun kasar Portugal wadda Cristiano Ronaldo yake jagoranta.