CRI Hausa" />

Kasar Masar: Yada Labaran Karya Game Da Xinjiang Da Masu Adawa Da Kasar Sin Ke Yi Yunkuri Ne Na Hana Ci Gaban Kasar

A kwanan nan, wasu masu adawa da kasar Sin na Amurka da na yammacin duniya sun yada labaran karya game da jihar Xinjiang a bayyane, sun kirkiri karya kan batutuwan da suka shafi Xinjiang kamar “Laifukan cin zarafin bil Adama” da “kisan kare dangi” da dai makamantansu, da nufin yin batanci ga nasarorin ci gaban da Xinjiang ta samu, da kuma gurgunta zaman karko da bunkasuwar jihar. ‘Yan jami’yyu daban daban na kasar Masar sun maida hankali kan batun tare kuma da yin Allah wadai da zarge zargen.
Mamban ofishin siyasa na jam’iyyar kwaminis ta kasar Masar Hassan Badawy ya bayyana cewa, ya taba zuwa kasar Sin, duk da cewa bai taba ziyartar jihar Xinjiang ba, amma wasu daga cikin abokan aikinsa sun taba ziyartar wajen, sun ba shi labarin abubuwan da suka gani a Xinjiang, kuma sun yi farin ciki da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali da jama’ar jihar ke ciki. Daga shekarar 2014 zuwa ta 2019, yawan GDP na Xinjiang ya karu daga RMB yuan biliyan 919.59 zuwa yuan biliyan 1359.71. Dangane da wannan yankin, adadin yana da ban mamaki, kuma yana kara tabbatar da irin himmar da jama’ar jihar Xinjiang suke, wadda ke da kabilu masu yawa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Exit mobile version