A ranar Laraba, ministar harkokin kiwon lafiyar kasar Peru Pilar Mazzetti ta ce, kasarta ta yarda da farfado da gwajin allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, wadda kamfanin harhada maganguna na kasar Sin wato Sinopharm ya taba farawa.
A makon da ya gabata, kasar Peru ta dakatar da gwajin da aka yi kan mutane 12,000, saboda daya daga cikinsu ya gamu da matsalar rashin lafiya, daga bisani, wani kwamitin likitoci ya gaskata cewa, rashin lafiyar jikinsa ba shi da alaka da alluar rigakafin.
Sa’an nan, ministar harkokin kiwon lafiyar kasar ta sanar da cewa, yanzu, gwamnatin kasar tana neman farfado da shawarwarin sayen allurar ta kamfanin Sinopharm. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)